Mutumin da ke rayuwa da dabbobi 400 a gidansa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mutumin da ke rayuwa da macizai da kadoji 400 a gidansa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Philippe Gillet wanda gidansa ke gabar kogin Loire a Faransa, na rayuwa da dabbobi masu jan ciki 400 a gidansa.

Yana da wasu kadoji biyu da ke yawonsu a falonsa da kuma wani kumurcin maciji a kan teburinsa da dai sauran dabbobi.

"Ina ga bai kamata mu dinga tafiyar da dabbobi irin yadda muke yi ba saboda ba mu fahimce shi ba," kamar yadda Gillet ya ce a wata hirarsa da Reuters.

Labarai masu alaka