Abin da ba ku sani ba kan rikicin 'yan awaren Kamaru

Red Dragons video screengrab Hakkin mallakar hoto Red Dragons

Kungiyoyin Red Dragon da Ambazonia Defence Forces (ADF) - na cikin kungiyoyin da suka dauki makamai domin yakin neman 'yancin yankin masu amfani da turancin Ingilishi daga Kamaru.

Sun kasance wata babbar barazana ga zaben shugaban kasa da za a yi ranar Lahadi, zaben da Shugaba Paul Biya mai shekara 85 da haihuwa ke neman tsawaita wa'adin mulkinsa na shekara 36.

Kungiyoyin masu daukar makamai da suka bulla shekara daya da ta gabata, sun karbe ikon garuruwa da kauyukan yankin masu amfani da harshen Ingilishi na arewa maso yamma da kudu maso yamma daga hannun gwamnatin Kamaru.

Wannan abu ne da shekaru biyun da suka gabata ana iy cewa ba mai yiwuwa ba ne, inji Nna-Emeka Okereke, wani mai nazarin siyasar Kamaru:

"Suna da kimanin mayaka 500 zuwa 1,000, amma abu mafi muhimmanci shi ne suna da karfin gwuiwar gudanar da yakin neman 'yancin wani yanki da suke kira Ambazoniya.

'Muna alfahari da amfani da turancin Ingilishi'

Kungiyoyin mayakan sun fara samuwa ne a 2017 bayan da sojojin Kamaru suka dakile wata zanga-zangar mutanen yankin, wanda lauyoyi da malaman makaranta suka jagoranta.

Sun tuhumi gwamnatin kasar da danne 'yan asalin yankin, kana tana fifita masu amfani da harshen Faransanci wajen samar da ayyuka da guraben ilimi.

Kashi 20 cikin 100 na al'ummar Kamaru sun fito ne daga yankin masu amfani da harshen turancin Inglishi.

Bayan da wasu kungiyoyi suka ayyana 'yancin kai a ranar 1 ga watan Oktobar 2017, gwamnatin Kamaru ta yi watsi da kudurin nasu, kuma ta kira su 'yan ta'adda, kuma tashar rediyon Kamaru ta ce Shugaba Biya ya ce zai yake su.

Image caption Yawancin 'yan yankin turancin Ingilishi sun ce ba a daukesu cikakkun 'yan Kamaru ba

'Yakin sunkuru ake yi'

Saboda dukkan kafofin gudanar da rayuwa mai ma'ana sun kafe, sai direbobin tasi a garin suka hana jami'an gwamnti shiga yankin, bayan da suka kafa wata kungiya mai suna Seven Karta militia - "karta" wani shahararren zani ne da mutanen yankin kan daura, kuma kalmar bakwai da ke cikin sunan na nufin wasu mutum bakwai ne da aka ce wai sun gagari turawan mulkin mallaka a wancan zamanin.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce suma 'yan awaren sun aikata laifukan take hakkin dan Adam.

Ban da kashe jami'an tsaro da suke yi, sun kuma rika kai wasu hare-hare "domin cusa tsoro a zukatan al'umomin kasar, har ta kai ga sun rika konamakarantu da kai hari kan malamai da suka ki kauracewa koyarwa", inji Amnesty.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda Kamaru ke kara fadawa cikin yakin basasa

Kungiyar kasa-da-kasa ta International Crisis Group (ICG) ta kiyasta cewa akwai kungiyoyin mayaka 10 masu neman a raba kasar a yankunan arewa maso yamma da na kudu maso yammacin kasar.

Kamaru - Ana tre amma kawuna na rarrabe:

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Turawan mulkin mallaka sun yi watandar nahiyar Afirka
  • Jamus ta fara mallakar Kamaru a 1884
  • Dakarun kasashen Birtaniya da Faransa sun fatattaki Jamusawa daga kasar a 1916
  • An raba Kamaru gida biyu bayan shekara uku - kashi 80 cikin 100 na Faransa, kashi 20 cikin 100 kuma na Birtaniya
  • Bangaren da Faransa ke iko da shi ya sami 'yanci a 1960
  • Bayan wani zaben raba gardama, yankin Kudancin Kamaru ya hade da Kamarun, inda yankin Arewacin Kamaru ya hade da Najeriya

Amma wata kungiy mai sa ido kan al'amuran da ke wanzuwa a kasar, Armed Conflict Location and Event Data (Acled), ta ce a shafinta na intanet kungiyar ADF ce mafi karfin iko a cikin dukkan

Kungiyar ta ADF ta fara kai hare-hare a 2017 ne a gundumar Manyu da ke yankin kudu maso yammacin kasar da Mezam da ke arewa maso yammacin Kamarun, kafin daga baya ta fadada ayyukanta.

Matsalar sai karuwa ta ke yi

Kungiyar ta ADF da ma sauran kungiyoyin mayaka sun kara da sojojin gwamnati sau 83 a cikin wannan shekarar kawai, idan aka kwatanta da yadda suka kara sau 13 kawai a bara, inji Acled.

Kungiyoyin sun kuma bude shafukan sada zumunta, inda kungiyar Red Dragons ke saka hotunan bidiyo na mayakanta, da suka hada da mata sanye da kayan yaki a cikin dazuzzuka, har ma da bidiyon yadda suka ce sun harbo wani jirgin helikwafta.

'Ba a tattaunawa domin sasantawa'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar ICG ta ce kawo yanzu an kashe sojoji da 'yan sanda 175 a Kamaru a dalilin yakin basasan

Yakin ya kuma yi sanadin rasa rayukan a kalla fararen hula 420, da 'yan sanda da sojoji 175 da daruruwan mayaka.

Fiye da mutum 30,000 kuma sun kauracewa muhallansu, inji kungiyar ta ICG.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana kallon Shugaba Paul Biya a mtsayin mai mulkin kama karya

Da alama Mista Biya ne zailashe zaben, domin shi ke da cikakken iko da sojoji da 'yan sandan kasar.

Amma tambaya a nan ita ce ko zai nemi sasantawa da kungiyoyin awaren bayan zaben.

Labarai masu alaka