Ziyarar Melania Trump a Ghana

Melania Trump paid a courtesy call on the local chief Osabarimba Kwesi Atta II before visiting the for Hakkin mallakar hoto DAILY GRAPHIC
Image caption Melania Trump ziyarci wani basaraken gargajiya Osabarimba Kwesi Atta II

Uwargidan shugaban Amurka Melania Trump na cikin rana ta uku ta ziyarar kasashen Afrika hudu da take yi ba tare da mijinta ba.

Ta fara ziyartar Ghana, inda ta leka wani wuri da ake ajiye bayi kafin a saka su a jiragen ruwan da suka tafi da su Amurka inda aka sayar da su kuma suka rayu a matsayin bayi.

Daga Ghana Misis Trump za ta ziyarci Kenya da Malawi da kuma Masar.

Shugaba Trump bai ziyarci nahiyar Afirka ba tun bayan zama shugaban Amurka a watan Janairun 2017.

Amma ziyarar da mai dakinsa ta kawo wani bangare ne na kokarin gyara barnar da kalaman Mista Trump suka yi ga dangantakarsa da Afirka.

Kafin mai dakin nasa ta bar Amurka, Mista Trump ya fada wa manema labaari cewa shi da ita na kaunar Afirka, kuma nahiyar ce bangaren wannan duniyar tamu mafi kayatarwa.

Amma kalaman nasa sun ci karo da wadanda ya furta a lokacin wani taro da yayi da jami'ansa a watan Fabrairu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan makaranta sun tarbe ta a birnin Accra

A wancan lokacin ya aibanta kasashen Afirka, kuma kalaman nasa sun janyo masa tarin matsaloli.

Batun ya kai ga sai da Tarayyar Afirka ta ce sai ya nemi kasashen Afirka su yafe masa, matakin da kawo yanzu bai dauka ba.

Ziyarar Misis Trump ba za ta wanke daudar wadancan maganganun da yayi ba, kuma idan yadda aka tarbe ta a Ghana wata manuniya ce, to lallai ba ta sami karbuwa ba ga mutanen nahiyar ba.

Labarai masu alaka