Abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da wasu 'yan Afirka a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Image caption 'Yan kabilar Oromo na kasar Habasha sun yi bikin Irreecha a ranar Lahadi. Sun yi kwalliya da tufafin gargajiya, mutane na dibar ciyawa zuwa tafkin Harsadi don nuna godiya ga Allah a farkon bazara.
Image caption Wasu matasa sun zabi wannan ranar ta zama ranar daurin aurensu. Angon ya ce yana murnar yin bikinsa a gaban duka mutanen da su ka fito bikin Irreecha.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya baya na murna a wata zanga-zangar adawa inda manyan 'yan takarar shugabancin kasar za su yi jawabi a gaban magoya bayansu, watanni uku kafin zaben da za a gudanar a ranar 29 ga Satumba, 2018 a birnin Kinshasa.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tallar kayan kawa suna shiryawa a bayan fage kafin su fito su yi tallar kayan a kasar Addis Ababa a makon tallar kayan kawa , ranar 3 ga watan Oktoba shekarar 2018.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ranar Alhamis, ma'aikata a wata masana'anta a Tunisiya su na warewa tare da busar da barkono wanda za a yi amfani da shi wajen sarrafa yajin Harissa, a ranar 3 ga watan Oktobar 2018.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata na dauke da lemu da ruwan sayarwa a kan kawunansu su na kallon ayarin motocin 'yan jaridar da ke harhada labarin ziyarar matar shugaban Amurka MelaniaTrump a Accra, Ghana ranar 2 ga watan Oktoba, 2018.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kasar Malawi na rike da tutoci yayin da matar shugaban Amurka Melania Trump ta isa Lilongwe a kasar Malawi a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba, 2018.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yara a babban birnin Kenya, Nairobi, suna nishadantarwa ta hanyar wasan kwaikwayon Tinga Tinga a ranar Jumma'a, 28 ga watan Satumba, 2018.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A rana guda a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu, masu rawar Ballet na shirin yin rawar ran 4 ga watan Oktoba, 2018
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dan macukule sanye da kaya masu siffar giwa na nishadantar da magoya bayan kwallon kafa a rufaffen filin wasan kwallon na Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a Abidjan, babban birnin Ivory Coast.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba, 2018 an kona tarin hauren giwa a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo a wani yunkuri na hana kashe giwa ba a bisa ka'ida ba.

Hadin mallakar hotuna AFP, EPA, Reuters and Getty Images.

Labarai masu alaka

Labaran BBC