Kamaru na zaben shugaban kasa

Zaben shugaban kasa a Kamaru Hakkin mallakar hoto Getty Images

Al'ummar Kamaru na shirin kada kuri'ar zaben shugaban kasa wanda za a gudanar cikin barazanar tsaro a yankin da ke magana da Inglishi.

Shugaba Paul Biya wanda ya shafe shekaru 36 kan mulki, kuma mutum na biyu da ya fi dadewa yana shugabanci a Afrika, zai fafata ne tsakaninsa da 'yan takara bakwai da ke adawa da shi.

Sai dai kuma rikicin 'yan a-ware wanda ya mamaye yankuna biyu na kasar da ke amfani da Turancin Ingilishi shi ne babbar barazana a zaben, inda 'yan a-waren suka bukaci mutanen yankin su kauracewa zaben bayan tun da farko sun yi barazanar hana gudanar da shi.

Amma Gwamnatin Kamaru ta yi wani babban gargadi ga duk wanda ya nemi ya dagula zaben shugaban kasar.

Gargadin kuma martani ne ga barazanar da 'yan a-waren Ambazonia suka yi a yankin da ke Magana da Inglishi kafin zaben.

Kafin fara kada kuri'a, jamai'an zaben sun sanar da cewa runfunan zaben da dama a yankin arewa maso yammaci da kudu masu yammaci da ke magana da Ingilishi za su kasance a rufe saboda barazanar tsaro.

Gwamnati ta tura Karin rundunar soji domin tabbatar da tsaro a zaben.

Shugaba Paul biya mai shekara 85 yana neman a sake zabensa a wani wa'adin shugabanci ne na bakwai.

Wasu manyan masu adawa da shi sun sanar da hade kai, inda dan takara Akere Muna mai da'awar yaki da rashawa ya sanar da janye takararsaa a ranar juma'a kuma ya sanar da marawa Maurice Kamto baya tsohon jami'in gwamnatin Biya.

Ana sa ran rufe runfunan zabe da misalin karfe shida na yamma agogon kasar.

Kuma bisa tsarin doka, hukumomin zaben na Kamaru na da tsawon mako biyu su bayyana sakamakon zaben.

Labarai masu alaka