Hotunan ziyarar Melania Trump a Afirka

U.S. first lady Melania Trump feeds a baby elephant a bottle of milk at the David Sheldrick Wildlife Trust elephant orphanage in Nairobi, Kenya, October 5, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Juma'a 5 ga watan Oktoba Melania Trump ta ziyarci gidan marayun dabbobi a Kenya, inda har ta shayar da wata jaririyar giwa madara a bulumboti. An ba ta giwa daya don ta raine ta.

Uwargidan shugaban Amurka Melania Trump ta ziyarci Ghana da Malawi da Kenya da kuma Masar domin habaka walwalar yara, a bulaguronta na farko zuwa kasashen waje da ta yi ita kadai.

Shugaba Donald Trump bai taba kai ziyara Afirka ba tun hawansa mulki a watan Janairun 2017.

A watan Fabrairu wani ce-ce-ku-ce ya barke bayan da aka yi zargin cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana kasashen Afirka da cewa "kasashen banza ne."

Ana ganin ziyarar Melania a matsayin wani kokari na magance rarrabuwar kawunan.

U.S. first lady Melania Trump takes a safari in Nairobi, Kenya, October 5, 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanya farar hular kwanon da matar shugaban Amurkan ta yi a Kenya ya jawo suka. Wasu da dama na ganin sanya hular a matsayin alama ta tunawa da mulkin mallakar da Turawa suka yi a karni na 19 a Afirka.
US First Lady Melania Trump receives flowers during an arrival ceremony after landing at Kotoka International Airport in Accra October 2, 2018 as she begins her week long trip to Africa to promote her 'Be Best' campaign. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ta fara ne da ziyartar birnin Accra na kasar Ghana a ranar Tallata, inda ta sha shayi tare da uwargidan shugaban kasar Ghana ta kuma ziyarci wani asibiti.
Women carrying drinks on their heads watch as the motorcade that carries the media covering U.S. first lady Melania Trump passes in Accra, Ghana, October 2, 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ga alama wadannan matan ba su nuna wani mamakinsu ba a lokacin da tawagar motocin da matar Trump ke ciki suke wucewa ba a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Ta ziyarci tsohuwar tashar jiragen ruwan da ake cinikin bayi a washe garin ranar da ta isa birnin. An dauke ta wannan hoton ne a gaban kofar da ake yi wa lakabi da "Door of No Return" wato kofar da ba dawowa - inda nan ne waje na karshe da bayin Afirka ke bi a yayin da za a kai su Amurka. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ta ziyarci tsohuwar tashar jiragen ruwan da ake cinikin bayi a washe garin ranar da ta isa birnin. An dauke ta wannan hoton ne a gaban kofar da ake yi wa lakabi da "Door of No Return" wato kofar da ba dawowa - inda nan ne waje na karshe da bayin Afirka ke bi a yayin da za a kai su Amurka.
a kuma je gabar tekun Atlantika inda ta nan ake tafiya da bayin. Ta ce "Tabbas abun da ya faru shekaru da dama da suka gabata babban tashin hankali ne." Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ta kuma je gabar tekun Atlantika inda ta nan ake tafiya da bayin. Ta ce "Tabbas abun da ya faru shekaru da dama da suka gabata babban tashin hankali ne."
Kamar dai sauran matan shugaban kasa, Melania Trump ita ma ta zabi amfani da damarta wajen tattauna batutuwan da suka shafi yara. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamar dai sauran matan shugaban kasa, Melania Trump ita ma ta zabi amfani da damarta wajen tattauna batutuwan da suka shafi yara.
Za ta kammala ziyarar da take yi din cikin kasa da mako daya. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za ta kammala ziyarar da take yi din cikin kasa da mako daya.
Uwargidan shugaban Malawi Gertrude Maseko ta tarbi takwararta ta Amurka a ranar Alhamis. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Uwargidan shugaban Malawi Gertrude Maseko ta tarbi takwararta ta Amurka a ranar Alhamis.
Ziyarar Melania a Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Melania Trump ta gana da yara a wata makarantar firamare a Lilongwe babban birnin Malawi.
Ziyarar Melania a Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Melania tana kallon yadda ake koyar da wasu yara a wata makaranta a Malawi
Ziyarar Melania a Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Masar kuwa, Uwargidan Trump din ta ziyarci dalar Giza a Alkahira
Ziyarar Melania a Afirka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ta kuma dauki hoto sanye da malafar Panama, a gaban gunkin Sphinx
Ziyarar Melania a Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matar shugaban Masar Intissar Amer al-Sisi ta yi wa Mrs Trump maraba a birnin Alkahira.

Hotuna daga AFP da Reuters

Labarai masu alaka