Hadarin mota ya yi ajalin mutum 50 a Kenya

Taswira na nunabirnin Nairobi da Kisumu da ke Kenya
Image caption Taswira na nuna birnin Nairobi da Kisumu da ke Kenya

'Yan sanda sun ce akalla mutum 50 ne su ka mutu bayan da wata motar bas da ke tafiya daga babban birnin kasar Kneya, Nairobi zuwa Kisumu, da ke yammacin kasar, ta kauce hanya.

Rahotanni sun ce yawancin mutanen sun rasa rayukansu bayan da motar ta jirkice.

'Yan sanda na ganin cewa yawan wadanda su ka mutu na iya karuwa, saboda yiwuwar cewa akwai sauran fasinjojin da suka makale a cikin motar.

"Rufin motar ya bare," inji wani jami'i.

'Yan sanda sun ce motar ta kufcewa direban ne, sai ya gangara cikin wani kwari a daidai wani sanannen wuri da hadurra ke yawan afkuwa.

Shugaban 'yan sandan Kasar, Joseph Boinnet, ya shaidawa gidan rediyon Capital FM cewa abin takaici ne da a ka rasa rai 51.

Rundunar 'yan sanda sun ce motar bas din na dauke ne da fasinjoji 52 a lokacin hadarin, wanda ya faru da safiyar Laraba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rufin motar ya bare bayan da bas din ta jirkice

Cikin wadanda suka muta harda kananan yara.

Jaridar Daily Nation ta ruwaito cewa wani wanda ya shaida al'amarin ya ce ya jiyo wata kara mai karfi.

Jaridar ta kara da cewa an kai mutane da yawa asibitin da ke yankin.

Manyan hanyoyi a Kenya dai na da hadari, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Kenya na cikin jerin kasashen da ke da hanyoyi masu cike da hadari.

A watan Disambar bara, mutane 36 ne su ka mutu a wani hadari inda manyan motoci biyu su ka yi taho mu gama a hanyar Nairobi kusa da garin Miga a Kenyar.

A shekarar 2016, motoci da dama ne su ka ci da wuta a wani hadarin da tankar mai ta haddasa a Naivasha, wanda mutane da dama su ka mutu.

Labarai masu alaka

Karin bayani