Mummunar guguwa ta sake afka wa Amurka da Indiya

Birnin Panama na Florida na cikin yankunan da suka shafi wannan iftila'in Hakkin mallakar hoto AFP/getty images
Image caption Birnin Panama na Florida na cikin yankunan da suka shafi wannan iftila'in

Wata guguwa irinta mafi karfi a tsawon shekaru da ake dakonta a kudu maso gabashin Amurka ta rage karfi bayan isarta Florida, sai dai ana saran za ta ci gaba da zama barazana.

Guguwar ta Hurricane Micheal da ta doshi Florida da karfinta ta karya bishiyoyi tare da haddasa iska da ke tafiyar kilomita 250 a sa'a guda.

Rahotanni sun ce akwai mutum guda daya mutu bayan faduwar wata bishiya a kan gidansa.

Gwamnan Florida Rick Scott, ya ce al'ummomin da ke zaune a yankunan gabar ruwa za su fuskanci mummunar asarar da basu taba tsammani ba.

Mista Scott ya kuma ja hankali a kan barnar da irin wannan guguwa ke haifarwa la'akari da abin da ya faru a lokacin Hurricane Irma.

Kusan mutum dubu 200 guguwar ta katsewa wutar lantarki, ko da dai akwai yi wuwar karuwar alkaluman yayin da guguwar ta doshi Georgia da Carolina.

A Indiya ma dai, guguwar ce mai karfin gaske ta afka wa jihar Odisha da ke gabashin kasar, sannan ta na tafe da karfin iska mai gudun kilomita 150 a sa'a guda.

Guguwar da aka bayyana da Titli, ta haddasa ruwan sama kamar da bakin-kwarya a fadin jihar da kuma hana tashin jiragen kasa da na Sama, da gudanar da ayyuka a manyan tashohin ruwa.

Mahukunta sun kwashe sama da mutum dubu 300 akasari masunta, guguwar ta yi tasiri sosai a gabashin Indiya, an kuma samu katsewar wutar lantarki ta kuma lalata dukkanin gidajen da ke kusa da gabar ruwa.

Tuni dai aka samar da matsugunai na wucin-gadi sama da dari 800 da kuma umartar mutane su zauna a gidajensu

Labarai masu alaka