Obasanjo ya goyi bayan Atiku a zaben 2019

Atiku ya ci abincin rana tare da Olusegun Obasanjo Hakkin mallakar hoto Twitter/Atiku Abubakar
Image caption Atiku ya ci abincin rana tare da Olusegun Obasanjo a Abeokuta ranar Alhamis

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gana da tsohon mai gidansa Cif Olusegun Obasanjo kuma sun ci abincin rana tare a garin Abeokuta na jihar Ogun.

Ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, kuma ya wallafa hotunansa tare da Obasanjo da malamin addinin Musulunci Dr Ahmad Gumi da malamin addinin Kirista Bishop Mathew Hassan Kuka wadanda ake zaton tare aka yi ganawar da su.

Hakkin mallakar hoto Twitter/Atiku Abubakar
Image caption Atiku ya gana da Cif Olusegun Obasanjo da Sheikh Ahmad Gumi da Bishop Matthew Hassan Kukah a ranar Alhamis

Atiku Abubakar ne ya yi wa Olusegun Obasanjo mataimaki lokacin da yake shugaban najeriya tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Tun bayan nan, dangantakar da ke tsakaninsu ta yi tsami kuma Obasanjo bai taba goyon bayan Atiku Abubakar ba a duk lokutan da ya fito a baya na nuna son yin shugabancin Najeriya.

An taba ruwaito Obasanjo yana cewa "zai yi iya bakin kokarinsa don ganin Atiku Abubakar bai shugabanci Najeriya ba."

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Atiku Abubakar, ya ce "Obasanjo ba shi ne Allah ba, kuma ba shi ne mutanen Najeriya ba."

Olusegun Obasanjo dai na daya daga cikin masu fada a ji a fagen siyasar Najeriya.

Kuma ya nuna goyon bayansa ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya lashe zaben 2015, sai dai a bana ya ce ba ya goyon bayan shugaban ya nemi wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.