Sulhunta Atiku da Obasanjo na je yi — Gumi

Sheikh Gumi a yayin sulhunta Atiku da Obasanjo Hakkin mallakar hoto TWITTER/ATIKU ABUBAKAR

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, daya daga cikin malaman addinan da suka shaida sasantawar tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a zaben 2019 wato Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ya yi karin haske a game da sasantawar da suka halarta.

Sheikh Gumi, ya shaida wa BBC cewa, shi dai an gayyace shi ne domin ya zama shaida a sulhun da aka yi tsakanin Atiku Abubakar da kuma Obasanjo.

Malamin addinin Islaman, ya ce an zabe su su je sulhun ne saboda ana neman mutanen da ba ruwansu da bangaranci addini kawai suka sanya gaba, shi ya sa yakasance daya daga cikin masu sulhun.

Sheikh Gumi ya ce, sun zama shaida a sulhun da aka yi ne, bisa la'akari da cewa duk wani abu da zai kawo sulhu a addinin musulunci, abu ne wanda aka kwadaitar da shi a yi shi.

Malamin addinin Islaman, ya kuma yi karin haske a kan zargin da ake cewa ko suna nuna goyon bayansu ne ga takarar Atiku Abubakar, inda ya ce ' Ba a Atiku Abubakar ba, ko wanene koda a misali shugaba Muhammadu Buhari zai fito ya ce zai yi sulhu da kanal sambo Dasuki da aka kulle, a nemi ni a ce na zo nayi sulhi, to zan yi'.

Sheikh Gumi ya kuma bayyana irin alfanun da ya ke ganin wannan sulhu na su Atiku da Obasanjo zai yi, inda ya ce abu na farko akwai rikici a kasar nan, yawanci kowa a cikin manyan kasar na ganin an cuce shi,to a irin hakan an bukatar yafiya don shi kasa ke bukata.

Malamin addinin ya ce, shi fa a bangarensa ba ya goyon kowa a takarar shugabancin kasa, domin ko iyalansa ma ba zai ce musu ga wanda za su zaba ba, don haka shi ba shi da zabi, kuma kowa na da na sa zabin.

Ga masu sha'awa, sai ku latsa alamar lasifika a hoton da ke kasa domin sauraron yadda hirar BBC da Dr Ahmad Gumin ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Dr Ahmad Gumi kan ziyarar da ya kai wa Obasanjo tare da Atiku Abubakar

Matashiya

Hakkin mallakar hoto TWITTER/ATIKU ABUBAKAR

A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gana da tsohon mai gidansa Cif Olusegun Obasanjo kuma sun ci abincin rana tare a garin Abeokuta na jihar Ogun.

Atiku Abubakar ne ya yi wa Olusegun Obasanjo mataimaki lokacin da yake shugaban najeriya tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Tun bayan nan, dangantakar da ke tsakaninsu ta yi tsami kuma Obasanjo bai taba goyon bayan Atiku Abubakar ba a duk lokutan da ya fito a baya na nuna son yin shugabancin Najeriya.

An taba ruwaito Obasanjo yana cewa "zai yi iya bakin kokarinsa don ganin Atiku Abubakar bai shugabanci Najeriya ba."

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Atiku Abubakar, ya ce "Obasanjo ba shi ne Allah ba, kuma ba shi ne mutanen Najeriya ba."

Olusegun Obasanjo dai na daya daga cikin masu fada a ji a fagen siyasar Najeriya.

Kuma ya nuna goyon bayansa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya lashe zaben 2015, sai dai a bana ya ce ba ya goyon bayan shugaban ya nemi wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.

Karanta wasu karin labaran