'Dalilinmu na auren bogi a Kinshasha a shafin Facebook'

Jean-Félix Mwema Ngandu and Arlene Agneroh sit side by side in matching outfits in this photo taken by a mutual friend who uploaded it to Facebook Hakkin mallakar hoto Christian Shabantu Mpenga
Image caption Hoton ya sa mutane ke tsammanin Arlene da Jean-Félix ma'aurata ne

Ga 'yan uwanta da abokan arziki, Arlène Agneroh ta taki sa'a, domin arzikin da ta mallaka na ilimi da abin hannu.

Arlène ta mallaki abin hannunta, tana kuma da ilimi, sannan ga kyau Allah ya ba ta. Mutane na kiranta shugaba - domin tana koyar da 'yan kasuwa hanyoyin samun nasarori a ayyukansu. Abu daya da mutane ke ganin ta rasa a rayuwarta shi ne miji.

Kwannan wan abu ya auku da ya ankarad da ita irin matsin da matasa ke fuskanta wajen yin aure a Jamhuriyar Deomradiyyar Kongo.

An gayyaci Arlene mai shekara 33 zuwa wani daurin aure a Kinshasa, babban birnin kasar ta Kongo - gayyata ta 30 da aka aika mata a cikin wannan shekarar kawai.

Kamar yadda lamarin ya zama al'ada a wajen bukukuwan daurin aure a kasar Kongo, dukkan bakin da amarya ta gayyata kan sanya kaya bai daya, wato 'anko', inda su kuma wadanda ango ya gayyata kan sanya nasu ankon.

A wajen bikin Arlene ta zauna kusa da wani abokinta mai suna Jean-Félix Mwema Ngandu.

'Abin tamkar hauka'

Ba tare da wata manufa ta daban ba, sai wani ya dauki hotonsu suna zaune kusa da juna a wajen bikin, kana ya saka hoton a shafinsa na Facebook.

Minti biyar bai wuce ba sai wayarsa ta fara kara. Kawai sai ya fara dariya.

"Me ke faruwa?", Arlene ta tambaye shi.

Sai ya sanar da ita cewa, "Wai mutane na tsammanin kun yi aure ne!"

Arlene Agneroh ta fada wa BBC daga baya cewa, "Lamarin tamkar wutar daji ya zama. Cikin mintuna kadan, gomman mutane sun tofa albarkacin bakinsu akan hoton, kuma sun rika aika min da sakonnin taya murna.

A wancan lokacin aboka biyu sun dauki abin kamar wasa ne - saboda haka ne ma suka sake daukar wani hoton, akan 'karagar' da aka kebe wa ango da amarya.

Hakkin mallakar hoto Larissa Diakanua
Image caption Tsofaffin abokansu sun rika cewa suna son halartar bikin bayan da suka ga wannan hoton

A wannan karon sun jira bayan wasu sa'o'i kafin duba yadda lamarin yake a shafin Facebook na wani abokin nasu na daban.

"Da na tashi kashegari da safe, sai naga daruruwan kiran da aka yi min a wayata, da sakonnin Facebook da na WhatsApp", inji ta.

Ta ce "Wasu sakonnin daga mutanen da na shafe fiye da shekara 10 ban yi magana da su ba ne. Ban san ma yadda wadannan mutanen suka sami lambata ba."

'Mutane na yarda da dukkan kwamachala a shafukan sada zumunta'

"Gaskiya idan ina magana akan ayyukan da nake yi, bana samun irin wannan martanin", inji Arlene.

Ta kuma ce, "Wannan ne gasiyar lamarin da muke ciki a halin yanzu, kuma sai ranar nan na tabbatar da haka."

Image caption Arlene ta ce aure ya kasance harkar gudanar da rayuwa a Kongo

"Lamarin ya sosa min zuciya saboda za ka ga ka kai wani mataki a rayuwa da kake ganin kana cikin farin ciki, amma sai mutane su matsa maka har ka fara tunanin ba haka lamarin yake ba."

'Har yanzu ina kasuwa'

Bayan da Arlene da Jean-Félix suka fara samun sakonnidaga abokansu da ke zaune a kasashen ketare suna nuna sha'awarsu ta komawa Kinshasa ta jirgin sama domin halartar "auren", sai Arlene ta ja layi, kana ta fallasa batun a nata shafin na Facebook.

Image caption Cocin Katolika na da karfin fada aji a rayukan mutanen Kongo, kuma fiye da rabin 'yan kasar mabiya darikarsa ce

A wani dogon bayani da ta wallafa, ta bayyana wa akawayenta da abokanta cewa: "Wadannan hotunan sun nuna wasu matasa biyu ne da abokansu suka dauki hotonsu, kuma babu inda aka bayyana cewa ma'aurata ne, amma dukkanku sai kuka zabi fassara hotunan a matsayin na ango d amarya."

"Ba tare da tambayar gaskiyar lamarin ba, kun rarraba hotunan, inda kuka kirkiri naku labarin. Saboda ku yanzu na fara rubuta sunayen wadanda zan gayyata zuwa aurena!"

"Amma a yanzu ga sako na a gareku, wadanda ke neman aurena amma suna fargabar sun rasa ni, to ina sanar da ku cewa har yanzu ina nan a kasuwa, sai dai ba a matse na ke da in yi aure ba."

"Saboda haka kuyi hakuri... Darasin da za ku koya shi ne kowa yayi tunani kafin ya dauki dukkan wani mataki a rayuwa. Domin hoto daya ba zai bayar da cikakken labari ba."

Cocin Katolika na da karfin fada aji a rayukan mutanen Kongo, kuma fiye da rabin 'yan kasar mabiya darikarsa ce.

Kashi 40 cikin 100 na mata a kasar na yin aure kafin su kai shekara 18 da haihuwa, kamar yadda alkaluman hukumar UNICEF ke bayyanawa.

Arlene ta ce "A nan kasar mutane na kallon aure a matsayin wani abin albarka ne."

"Kana iya samun saurayi ciki wata biyu sai ya fara maganar aure. Kuma wannan na shanye kawunan 'yan mata da yawa"

Image caption An rarraba wannan hoton sau da dama ba tare da bincike ba