Lost ancient city rediscovered with lasers
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An gano birnin Kweneng na Afirka ta Kudu da kasa ta binne da fasahar zamani

Masana ilimin tarihi sun yi amfani da fasashar hasken laser wajen gano wani tsohon birni a wajen birni mafi muhimmanci a bangaren kasuwanci a Afirka ta Kudu wato Johannesburg.

Birnin wanda dadadde ne, wanda ake ganin yayi tashe tun karni na 15, ya kasance mazaunin 'yan kabilar Tswana su kusa da 10,000.

Jikokinsu na cewa ya kamata hukumomin kasar su ayyana Kweneng a matsayin kasarsu ta asali.

Wadanda suka hada bidiyon: Glenn Middleton da Nomsa Maseko da Vauldi Carelse.

Labarai masu alaka