2019: Ba za mu canja Peter Obi a matsayin mataimakin Atiku ba – PDP

Atiku Hakkin mallakar hoto PDP
Image caption Atiku Abubakar ne dan takarar shugabancin Najeriya a PDP a zaben 2019

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce ba ta fuskantar matsin lamba bayan tsayar da Mista Peter Obi a matsayin dan takarar mataimakin shugabancin kasar a zaben 2019.

Ike Abonyi shi ne mai magana da yawun Shugaban jam'iyyar Uche Secondus kuma ya shaida wa BBC cewa jam'iyyar ba za ta sauya Peter Obi ba.

Wannan ya biyo bayan wani taro ne da shugabannin jam'iyyar da gwamnonin shiyyar kudu maso gabas wato yankin da Peter Obi ya fito suka yi, inda suka ce babu wani da ya tuntube su gabanin fitar da sunansa.

Mista Ike ya ce abin da gwamnonin suka fadi ba zai sa jam'iyyar ta sauya zabin da ta yi ba.

"Dan takarar shugabancin kasa ne da kansa yake zaben wanda zai rufa masa baya a zabe," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Wannan ba magana ce da gwamnonin za su fito su fada wa duniya ba, magana ce da ta kamata a yi ta a asirce."