Matar da ta kashe kanta da 'ya'yanta saboda mutuwar karyar mijinta

A picture of the husband and wife that has been circulating on Weibo Hakkin mallakar hoto Weibo
Image caption A farkon watan Satumba ne Mista He ya sayi tsarin inshora kan kudi dala 145,000 ba tare da sanin matarsa ba

Wani mutum wanda matarsa ta kashe kanta tare da 'ya'yanta bayan da aka yi zargin cewa ya kitsa mutuwarsa da gangan saboda a biya shi kudin inshora, ya mika kansa ga 'yan sanda a kasar China.

An zaci mutumin mai shekara 34 ya mutu ne bayan da aka gano motarsa a kogi, duk da cewa dai ba a ga gawarsa ba.

Bai gaya wa matarsa shirinsa na mutuwar karyar ba, don haka ta yi amanna cewa ya mutu.

Daga bisani sai ta fada cikin kududdufi tare da 'ya'yanta bayan da ta wallafa sakon cewa za ta kashe kanta a intanet.

Mutumin, wanda 'yan sanda suka ce sunansa He, ya mika kansa ga 'yan sandan ne a gundumar Xinhua a makon da ya gabata.

A wata sanarwa da 'yan sanda Xinhua suka fitar a kafar WeChat sun ce an tsare shi kan tuhumar zambar inshora da kuma lalata dukiya ta kasa da kasa.

A farkon watan Satumba ne Mista He ya sayi tsarin inshora kan kudi dala 145,000 ba tare da sanin matarsa ba, a cewar 'yan sanda.

A cewar wani rahoto da gidan rediyon gwamnatin China ya fitar, sunan matarsa ya sa a matsayin wacce za ta ci gajiyar inshorar.

'Yan sanda sun ce a ranar 19 ga watan Satumba, Mista He ya yi amfani da wata mota da ya ara don shirya yadda mutuwar karyar tasa za ta kasance.

An gano cewa ana bin sa bashin kudin kasar yuan 100,000.

A ranar 11 ga watan Oktoba ne kuma aka gano gawar matar tasa mai shekara 31 da dansu mai shekara hudu da kuma 'yarsu mai shekara uku a wani kududdufi kusa da gidansu, a cewar gidan rediyon Muryar China.

A wani sako da ta wallafa a WeChat, ta rubuta cewa ga ta nan za ta bi bayan mijinta, inda ta kara da cewa "yanzu na kara jin ina so mu kasance tare a matsayin iyalai mu hudu har abada."

A washe garin ranar ne Mista He ya mika kansa ga 'yan sanda.

Tun da fari dai ya wallafa a shafinsa na bidiyo, wanda daga baya aka yi ta yadawa, inda yake kuka yana cewa ya ranci kudi don ya biya kudin maganin 'yarsa, wacce ke fama da farfadiya.

An yi ta yayata zancen a kafafen sada zumunta na China a makon da ya gabata, inda ya jawo ce-ce-ku-ce kan yadda iyalai ke fama da matsalar rashin kudi da nauyin iyali.

An yi ta amfani da maudu'in #ManFakesDeathLeadingtoWifesDeath sau kusan miliyan 29 a kafar intanet ta Weibo.

Labarai masu alaka