Yadda Paul Biya ya sake lashe zaben shugaban Kamaru

Cameroon's President and head of Cameroon People's Democratic Movement Paul Biya speaks to media after casting his vote at a polling station during presidential elections in Yaounde, Cameroon on October 07, 2018. Hakkin mallakar hoto Anadolu Agency/Getty Images
Image caption Tun shekarar 1982 Shugaba Biya mai shekara 85 yake mulkin Kamaru

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya lashe zaben kasar a karo na bakwai a wani zabe da mutane da dama ba su fita kada kuri'a ba da kuma tsangwamar masu kada kuri'a da aka dinga yi.

Mista Biya mai shekara 85, wanda shi ne shugaban kasar da ya fi tsufa a Afirka, ya lashe zaben ne da kashi 71.3 cikin 100, a cewar sakamakon da jami'ai suka fitar.

'Yan jam'iyyun adawa sun yi kira da a yi zagaye na biyu na zaben, sai dai Hukumar Kundin Tsarin Mulki ta ki yarda da hakan a makon da ya gabata.

An girke 'yan sandan kwantar da tarzoma a ranar Lahadi a manyan biranen Yaoundé da Douala cikin shirin ko ta kwana na zanga-zangar 'yan adawa.

An shafe fiye da shekara guda ana fama da rikici a yankunan da ke amfani da Turancin Ingilishi biyu na Kamaru, da kuma hare-haren 'yan aware da suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Kwanaki biyu kafin a saki sakamakon, shugaban kasar Equatorial Guinea da ke makwabtaka da Kamarun wanda ya fi kowa dadewa a karagar mulki cikin shugabannin Afirka, Teodoro Obiang Nguema ya taya Mista Biya murna kan nasarar da ya yi.

Maurice Kamto na jam'iyyar MRC/CRM, ya samu kashi 14.2 cikin 100. Amma a birnin Doula Mista Kamto ya buge Mista Biya da rata mara yawa.

A fadin kasar kuwa, rabin mutanen da shekarunsu ya kai su kada kuri'a ne kawai suka yi zaben.

Dubun-dubatar mutane ba su samu damar kada kuri'a ba saboda matsalar rashin tsaro.

Barazanar barkewar rikici da 'yan tawaye ke yi ya sa masu kada kuri'a sun kasa yin zaben.

A ranar zabe kuwa dakarun tsaro sun harbe wasu 'yan aware uku da ake zargi da bude wa masu wucewa wuta.

Wasu 'yan tawaye sun yi kokarin kawo tarnaki a rabon kayan zabe inda suka haramta yin tafiya baki daya.

Kashi biyar cikin 100 ne kawai suka kada kuri'a a yankuna biyun da ke amfani da Turancin Ingilishi, a cewar Kungiyar Magance Rikici ta Duniya.

Alkaluman hukumomi sun nuna cewa kashi 16 cikin 100 ne suka fita zaben a yankin masu amfani da Ingilishi a Kudu maso Yammacin kasar.

Shaidu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun ji karar harbe-harbe a ranar Litinin da safe a Buea, babban birnin yankin masu Ingilishi da ke Kudu maso Yamma.

Hukumar zabe ta Kamaru Elecam ta kuma rage yawan rumfunan zabe a fadin yankin masu Ingilishi da ke Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, suka kuma mayar da wasu rumfunan yankunan da suka fi kwanciyar hankali daga wajen da ake fama da rikici.

Image caption 'Yan adawa sun shigar da kusan korafe-korafe 18 da aka yi na zaben don yin zagaye na biyu

'Yan adawa sun shigar da kusan korafe-korafe 18 da aka yi na zaben don yin zagaye na biyu, inda wasu ke zargin an yi zamba a Kotun Kundin Tsarin Mulki ta Kamaru, hukumar da ke da alhakin sanar da sakamakon, tun kafin ma a saki sakamakon.

Daga cikin masu kira da a sake sabon zabe har da manyan abokan karawar Mista Biya - Mista Kamto da Joshua Osih na jam'iyyar adawa ta SDF/FSD.

Mista Kamto dai har sai da ya ayyana kansa a mastayin wanda ya lashe zaben duk da cewa ba shi shaidar hakan.

Hakkin mallakar hoto Anadolu Agency/Getty Images
Image caption Mutane ba su fita kada kuri'a sosai ba

Masu sa ido daga Kungiyar Tarayyar Afirka sun ruwaito cewa an yi zaben lafiya, amma sun kara da cewa "mafi yawancin jam'iyyun ba su da wakilai" idan aka zo batun wa za a bari ya lura da yadda ake kada kuri'a da kuma kirga kuri'un a rumfunan zabe.

Kungiyar da ita kadai ce ta tura masu sa ido ita ce International Organisation of La Francophonie (OIF), wato Kungiyar Kasashe Rainon Faransa, wadda shugabanta ya bukaci masu ruwa da tsaki da 'yan takara su yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi komai lafiya, su kuma yi amfani da hanyoyin da shari'a ta tanada don kalubalantar sakamakon.

Tun da fari an sanya za a yi zaben 'yan majalisun dokokin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba tare da na shugaban kasa, amma sai aka daga zuwa shekarar 2019.

Labarai masu alaka