An kusa a fara gini da fitsarin dan Adam a Afirka Ta Kudu

From left: Dr Dyllon Randall and his students, Vukheta Mukhari and Suzanne Lambert holding the world’s first bio-brick made using human urine

Asalin hoton, Robyn Walker/UCT

Bayanan hoto,

Da farko bulon na warin sinadarin ammonia, amma ya kan daina wari bayan kwana biyu

Daliban wata jami'a a Afirka ta Kudu sun kirkiro wani bulo wanda ba ya illa ga muhalli wanda kuma aka hada da fitsarin dan Adam.

Daliban sun hada fitsari da yashi da kwayar halitta ta bakteriya wajen hada bulon, idan aka adana su a daki mai madaidaicin yanayi.

"Ana hada wannan bulon ne kamar yadda ake hadadutsen cikin teku," inji Dyllon Randall, wanda shi ne malamin da ke sa ido a kan aikin binciken da daliban a jami'ar Cape Town.

Wasu bulullukan kamar jan bulo na bukatar zafi domin a gasa su, lamarin da kan haifar da dumamar yanayi saboda yawan iskar carbon dioxide da ake fitarwa.

'Karfinsa kamar dutse'

Daliban masu nazarin kimiyyar hade-hade a jami'ar ta Cape Town (UCT) sun rika samun fitsarin da suke amfani da shi ne wajen tara fitsari a bayin maza.

Asalin hoton, UCT

Bayanan hoto,

Bulon na daukar kimanin kwana hudu zuwa shida kafin su sami karfi da inganci

A wajen hada bulon, da farko a kan sami takin zamani ne, kamin daga baya a yi amfani da sauran fitsarin wajen samar da abin da jami'ar ke kira "bulo da aka samu daga kwayoyin halitta".

Shin fitsari nawa a ke bukata a samar da bulo daya?

Asalin hoton, Getty Images

  • A duk lokacin da dan adam yayi fitsari, a kan sami tsakanin mil 200 zuwa 300 na ruwan fitsari
  • Irin wannan bulon na bukatar lita 25 zuwa lita 30 kafin ya iya girma - wasu za su ce fitsarin na da yawa sosai, amma yawancin fitsarin ana amfani da shi ne wajen samar da wani nau'in taki da yawansa ya kai kilo 1
  • Saboda haka hada bulo daya na bukatar mutum yayi fitsari sau 100.