Shahararriyar mawakiya Sinéad O'Connor ta Musulunta

Shuhada' Davitt, formerly known as Sinéad O'Connor

Asalin hoton, Twitter/@MagdaDavitt77

Bayanan hoto,

Mawakiyar ta ce ta yi farin ciki bayan da ta zama Musulma

Shahararriyar mawakiyar nan 'yar kasar Ireland Sinéad O'Connor ta bayyana karbar addinin Musulunci.

Mawakiyar wadda ta yi fice a shekarun 1990 da wakarta mai suna Nothing Compares 2 U, ta ce ta sauya sunanta zuwa Shuhada.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, mawakiyar ta gode wa Musulmi saboda goyon bayan da suke ba ta.

Ta kuma ce ta dauki matakin shiga addinin Musuluncin ne saboda gamsuwar da ta yi da shi bisa radin kanta.

A ranar Alhamis wani malamin addini a kasar Ireland Shaykh Dr Umar al-Qadri ya wallafa wani hoton bidiyon lokacin da mawakiyar ta karbi shahada.

Ba wanna ne karo na farko da mawakiyar wadda ta canja sunan zuwa Magda Davitt a bara ta yi maganar addininta a bayyane ba.

A shekarar 1992, ta jawo ce-ce-kuce bayan ta yage wani hoto da ke tallata wani shirin talabijin na Fafaroma a Amurka.