'Yan takara 78 ne za su kalubalanci Buhari

INEC Chairman Profesor Mahmood Yakubu
Bayanan hoto,

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar zabe ta Najeriya, INEC ta fitar da alkaluma da ke bayyana yawan 'yan takarar da jam'iyyun siyasar Najeriya suka mika mata a mukaman shugaban kasa da na 'yan majalisun kasa.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya gana da maneman labarai a Abuja.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ce 'yan takara 79 ne za su yi takarar mukamin shugaban kasa, inda ya ce 'yan takara 1803 ne za su fafata a zaben 'yan majalisar dattawa.

A matakin majalisar wakilai kuwa, ya ce 'yan takara 4,548 ne zasu yi takara.

Shugaban hukumar game da shirye-shiryen da ke gaban hukumar zaben ganin cewa majalisar kasar ta amince da ayar dokar zabe da shugaban Najeriya ya tura masu.

A cikin makon farko na shekara mai zuwa ne ake sa ran hukumar zaben za ta bayyana sunayen 'yan takarar mukaman gwamnonin jihohi da na 'yan majalisun jihohin kasar.

To game da takaddamar 'yan takarar jam'iyyar APC daga jihar Zamfara, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa ba ta karbi sunayen 'yan takarar ba.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC.