Amnesty ta yi tir da kashe Jamal Khashoggi

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International

Asalin hoton, Getty Images

To a yayin da batun kashe dan jaridar nan Jamal Khashoggi da hukumomin kasar Saudiya su ka yi a ofishin jakadanci Turkiyya ke ci gaba da daukan hankula a duniya, kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a cikin lamarin.

Kungiyar ta bakin mai magana da yawunta a Najeriya Isa Sunusi, ta ce kisan da aka yi wa dan jaridar akwai rashin imani da zalunci da kuma rashin sanin darajar ran dan Adam.

Isa Sunusi, ya shaida wa BBC cewa, idan har da laifi ya yi shi dan jaridar bai kamata ayi masa irin wannan kisan ba saboda akwai shari'a sai a hukunta shi dai-dai da laifin da ya aikata.

Amnesty ta ce, a yanzu babban abin da ta ke so ayi a kan wannan kisa da aka yi Mr Jamal, shi ne Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci bincike a kan wannan batu, sannan kuma duk wanda aka kama da hannu a kisan dan jaridar kowanene, a hukunta shi yadda yakamata.

Amnesty ta ce, yakamata mutane su sani cewa, 'yan jarida ba abokan gabar mutane ba ne, 'yan jarida mutanene da suke aiki mai cike da hadari domin su taimaka wa al'umma ta hanyar wayar musu da kai.

Amma kuma masu mulki a fadin duniya sai kara takurawa da musguna wa 'yan jaridar suke saboda basa so a gaya wa al'umma abinda suke inji Amnesty.

Karin bayani

Asalin hoton, Reuters

Gani na karshe da aka yi wa Mr Khashoggi, mai sukar gwamnatin Saudiyya a rubuce-rubucensa, ranar 2 ga watan Oktoba ne yayin da yake shiga ofishin jakadancin.

Rahotanni sun nuna cewa an far wa Khashoggi a ofishin bayan da ya shiga ya karbo takardun aurensa.

Majiyoyi a Turkiyya na ganin cewa wata tawagar karfafan mutane 15 masu kisa 'yan Saudiyya ce ta kashe shi, amma Saudiyyar ta dage a kan cewar ya fita daga ofishin cikin koshin lafiya.

A baya dai, Mr Khashoggi mai bai wa masarautar Saudiyya shawara ne kafin dangantakarsu ta yi tsami, inda daga baya ya yi gudun hijira na rajin kai.

Karanta wasu karin labaran