Saudiyya za ta hukunta mutanen da suka kashe Khashoggi

Saudi Arabia's Foreign Minister Adel bin Ahmed Al-Jubeir speaks during the second day of a conference in Manama, Bahrain.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Adel al-Jubeir ya ce mutanen da suka yi kisan sun keta doka

Ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce a cikin kasar za a hukunta mutanen da ake zargi da hannu a kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

A wajen taron da ya yi a Bahrain, Adel al-Jubeir ya zargi kafafen watsa labaran kasashen Yammacin duniya da kara gishiri game da batun kisan dan jaridar.

Ya yi tsokacin ne kwana guda bayan Turkiyya ta ce za ta kori 'yan kasar Saudiyya 18 wadanda hukumomi suka ce suna da hannu a kisan Khashoggi.

An kashe dan jaridar ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul mako uku da suka wuce.

Saudiyya ta musanta cewa masarautar kasar na da hannu a kisan inda ta dora alhakinsa kan wadanda ta kira "jami'an da basu iya aikinsu ba".

Tun da fari dai, mahukunta Saudiyya sun musanta masaniya kan kisan Jamala Khashoggi sai dai daga bisabi mai shigar da kara na kasar ya ce an kitsa kisan ne.

Khashoggi ya shahara wurin sukar yarima Mohammed, mai jiran gadon sarautar kasar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Jamal Khashoggi ya shahara wurin sukar yarima Mohammed, mai jiran gadon sarautar kasar.