Helikwafta ya yi hadari da mai Leicester City

Jirgi mai saukar ungulu mallakar mai kungiyar Leicester City

Asalin hoton, PETE WHITE

Jirgi mai saukar ungulu mallakin mai kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ya yi hadari a wajen ajiye motoci na filin wasan kungiyar jim kadan bayan tashinsa daga filin bayan kammala wasan Premier.

Mr Vichai Srivadana Prabha dai wato mai jirgin kuma mai kungiyar wasan kwallon kafar ta Leicester dai na cikin jirgin a lokacin da ya fado.

Wata majiya daga iyalan mai jirgin ta shaidawa BBC cewa Mr Vichai na cikin jirgin a lokacin da ya fado.

Asalin hoton, PA

Leicester City ta kara ne da kungiyar West Ham United a gasar Premier wadda aka yi a filin wasa na King Power stadium.

Hotunan da aka dauka na wajen sun nuna yadda wuta ke tashi sama a wajen ajiye motocin, amma daga baya an shawo kanta.

Asalin hoton, LIAM HOPKIN / @HOPKIN_LIAM

Wani mai sharhin wasan kwallon kafa na BBC Ian Stringer, ya ce jirgin na watan gariri a sararin samaniya ne kafin daga bisani kuma ya fado kamar dutse.

Ya ce yaga jami'an kungiyar da kuma mutane da dama na kuka.

Mr Vichai dai ya sayi kungiyar kwallon kafar ta Leicester City ne a shekarar 2010, kuma tun bayan siyan kungiyar ta dauki kofin gasar premier a 2016.

Shine dai mutum na hudu mafi arziki a Thailand a cewar mujallar Forbes.

Wani ganau ya ce farfelar jirgin ta baya bata juyawa wanda ya sa jirgin ya fara watangaririya har ya kai ga fadowa kasa.

Tuni dai 'yan kungiyar ta Leicester City da West Ham suka fara aika sakonnin twitter tun bayan faruwar lamarin.

Karanta wasu karin labaran