An kashe Yahudawa a wajen bauta

'Yan sanda a wajen da aka kai harin

Asalin hoton, Reuters

Mahukunta sun ce akalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wani harin bindiga da aka kai a wajen wani bauta na yahudawa da ke birnin Pittsburg da ke jihar Pennsylvania a Amurka.

Dan bindigar ya bude wuta ne a wajen bautar mai suna Tree of life na yahudawa inda daga baya kuma jami'an tsaro suka kama shi.

Shugaba Trump ya ce an kashe mutane da dama yayin da aka raunata wasu kuma a wani hari na keta.

Mutumnin da ake zargin wanda a hukumance aka bayyana shi da Robert Bowers mai kimanin shekara 46, ya ji rauni inda kuma ake masa magani a yanzu haka.

'Yan sanda sun ce mutane biyu na kwance a asibiti a halin rai kwakwai mutu kwakwai sakamakon harin da aka kai.

Masu bincike na hukumar FBI na kallon hari a matsayin laifi na nuna kiyayya.

Masu bautar sun taru ne a wajen bautar ta su a unguwar Squirrel Hill domin zagayowar ranar ibadarsu.

Unguwar Squirrel Hill na daya daga cikin wuraren da ke da yawan Yahudawa a jihar Pensylvania.

Kamar yadda rahotanni suka ambato, Mr Bowers wanda farar fata ne ya shiga wurin ibadar a ranar asabar dauke da bindigogi uku.

Rahotanni sun ce ya rufe kansa a wani daki da ke wajen bautar bayan da 'yan sanda suka isa wurin.

Ma'aikatan agaji dai sun isa wajen da karfe 10 na safiyar ranar kuma har wannan lokacin ana jin karar harbe harbe.

Wurin da aka yi abin dai ba bu kyan gani inji wani shugaban jami'an tsaro a jihar.

Jami'in ya ce an raunata wasu jami'an tsaro biyu a farkon da aka tunkari mutumin da ake zargin, sannan daga bisani wasu 'yan sandan kundun bala biyu sun ji rauni bayan da dan bindigar ya harbe su a lokacin da suka kutsa cikin ginin, sai dai kuma ba bu yara a cikin wadanda abin ya shafa.

Karanta wasu karin labaran