Abin da ya faru a Afirka makon jiya 19-25 October 2018

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da kuma wasu 'yan Afirka a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

The shadow of a helicopter seen in an area rich in diamonds in northern Angola - Saturday 20 October 2018

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kasa mai albarkar lu'u lu'u, a arewacin Angola, a kan iyakarta da Jamhuriyar Demokradiyar Kongo kenan ake iya gani daga jirgi mai saukar angulu a ranar Asabar...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A wannan ranar dai kuma jami'ai suka tilasta wa 'yan Congo fiye da dubu 300,000, har da wanan matar da su koma gida domin suna satar lu'u lu'u ba bisa ka'ida ba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Laraba, wani dillali a babban birnin Senegal wato Dakar, a lokacin da yake hutawa a kan kwale-kwalen wani masunci.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Larabar dai, aka dauki hoton Shugaban Senegal Macky Sall, a yayin da yake hira da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a lokacin wani taro a Riyadh, wanda ya gudana duk da zarge-zargen da ake yi wa Saudiyya na kisan dan jaridar nan Jamal Kashoggi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wasu maza 'yan kabilar Bedouin a yayin da suke kide-kide lokacin wani buki a yankin Sinai na kasar Masar a ranar Juma'a.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Bayan kwana uku, masu yawon bude ido a lokacin da suke daukar yadda hasken rana ke haskaka gunkin Ramses na biyu, a wani gidan bauta a kudancin Aswa. Wani gagarumin abu ne da ke faruwa sau biyu kawai a shekara.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Nice Nailantei Leng'ete, wata 'yar Kasar Kenya mai fafutuka game da kaciyar mata, a lokacin da take karbar kyautar girmamawa a ranar Asabar a wani bukin bayar da kyauta na Spaniya ---- .

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Asabar, wata mai tallar kayan kawa, a lokacin wani taron tallan kayan kawa na Afro Futuristic, wanda aka yi a Jami'ar Amurka ta Newa Hampshire...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wata dama mai kyau ce masu zanan kaya suka samu domin baza kayayyakinsu na Afirka da kuma samfuran dunkin da za a iya sawa daga nan har shekara dubu masu zuwa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Bukin makon tallan kayan kawa na Afirka ta Kudu da aka yi a Birnin Johannesburg a ranar Laraba shi ma da alama akwai yiwuwar ba za a daina yayin shi nan kusa ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Amma a Bamako babban birnin Mali, an yi bikin tallan kawa na duniya na WE WAX ne a ranar Asabar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sai kuma wani Jarumi da ba za a iya sharewa ba a fanin tallan kayan kawa, Frai Minista Ethiopia Abiy Ahmed a lokacin da ya iso majalisa da shigar birgewa a ranar alhamis. And not to be outdone on the fashion front, Ethiopia's Prime Minister Abiy Ahmed turns up in parliament looking dapper on Thursday.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yan kasar Kamaru a lokacin da suka saka atamfa wanda ke da fuskan Shugaban su Paul Biya a kai, a lokacin da suke nuna murnan cin zaben da yayi, a birnin Yaounde a ranar litinin. Cameroonians in material showing the face of President Paul Biya celebrate his election victory in the capital, Yaounde, on Monday.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Frisinonin kudancin Sudan a lokacin da suke fita a gidan yarin Birnin Juba a ranar alhamis, a cikin wani yarjejeniynar zaman lafiyan da aka kulla a watan da ya gabata. South Sudanese prisoners of war walk out of jail in the capital, Juba, on Thursday - as part of a peace deal signed last month.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar talata wasu maza a birnin Tunisia, a lokacin da suke kallon tallan wani fim din Papa Hedi, wanda aka sadaukar ga babban jarumin nan na wake wake Heidi Jouini, wanda jikar shi Claire take matsayin daraktan fim din. On Tuesday, men in Tunisia's capital, Tunis, look at a film poster for Papa Hedi, dedicated to the famous singer Hedi Jouini and directed by his granddaughter Claire.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wani matashi mai wasanin ruwa a lokacin da yake wasa da ruwa kusa da Cape Town dake Afrika ta kudu a ranar alhamis. A young surfer rides a wave at sunrise near Cape Town in South Africa on Thursday.

Bayanan hoto,

Magoya bayan wadda taci nasara a wani shirin telebiyon na Big Sister a lokacin da suke mata sowa yayin wani faratin da tayi a birnin Freetown a ranar alhamis. And fans of the winner of Sierra Leone's Big Sister reality TV show cheer her on as she takes part in a victory parade in the capital, Freetown, on Thursday.

Pictures from AFP, EPA, Reuters and Getty Images