Hotunan abubuwan da suka faru makon jiya: Shin Ganduje zai rantse da Alkur'ani?

Peter Ayodele Fayose

Asalin hoton, Twitter/@GovAyoFayose

Bayanan hoto,

Da safiyar Litinin ne hukumar EFCC da ke yaki da masu yi a tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ekiti Peter Ayodele Fayose a gaban wata kotun birnin Lagos bisa zargin cin hanci da rashawa.

Nasir Elrufai

Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna

Bayanan hoto,

Ranar Talata, Gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufai ya kai ziyara asibitin St. Gerards domin duba mutanen da suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke a wasu sassan jihar a makon jiya

Asalin hoton, Twitter/@dawisu

Bayanan hoto,

Ranar Laraba, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana kallon wasan karshe na cin kofin kalubale da kungiyar kwallon kafar Kano Pillars ta fafata da Enugu Rangers a talbijin...

Asalin hoton, Facebook/Jaafar Jaafar

Bayanan hoto,

...washegari, dan jaridar nan, Jaafar Jaafar, wanda ya fitar da bidiyon da ke zargin Gwamna Ganduje na karbar cin hanci daga wurin 'yan kwangila, ya bayyana a majalisar dokokin jihar Kano domin bayar da ba'asi. Ya sha alwashin rantsuwa da Alkur'ani inda ya kalubalanci gwamnan shi ma ya rantse

Asalin hoton, Twitter/@BashirAhmaad

Bayanan hoto,

...ranar Alhamis din ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon ginin hada-hadar fasinjoji a filin jirgin saman Fatakwal da ke jihar Ribas.

Asalin hoton, Twitter/@atiku

Bayanan hoto,

Ranar Juma'a dan takarar shugabancin Najeriya a PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya wallafa wannan hoton a shafukansa na sada zumunta inda ya ce yana sake bibiyar takardun da ke kunshe da kudure-kudurensa na yi wa kasar garambawul, wadanda zai gabatar wa 'yan Najeriya...

Bayanan hoto,

...da almurun ranar ne aka karrama taurarin gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bana