An sassauta dokar hana zirga-zirga a Kaduna

Kaduna

Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sake sassauta dokar hana zirga-zirga a birnin Kaduna da kewayensa.

Sanarwar da gwamnan jihar Nasir Elrufai ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi ta ce an sassauta dokar ne bayan an gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro.

A cewarsa, "Ranar Lahadi mazauna birnin za su iya yin zirga-zirga har zuwa karfe biyar na yamma. Daga Litinin, 29 ga watan Oktoba, mutane za su iya zirga-zirga daga shida na safe zuwa biyar na yamma.

"Ana sa ran kasuwanni da bankuna za su bude. Amma za a ci gaba da tsaurara dokar hana zirga-zirga da daddare," in ji sanarwar.

A karshen makon jiya ne aka sake sanya dokar hana zirga-zirgar a birnin na Kaduna da kewaye da kuma wasu yankunan karamar hukumar Kachia bayan kisan da aka yi wa ani basaraken da masu satar mutane suka sace.

Mutane da dama ne dai suka mutu tun daga makon jiya sanadiyar rikicin da aka yi a garin Kasuwan Magani da ke kudancin jihar.

Ko da a ranar Juma'a sai da wasu matasa a garin Gonin Gora da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka toshe hanya da zummar far ma matafiya.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai jami'an tsaro sun tarwatsa su.

Matasan garin sun sha tare matafiya suna kashe su da zarar an soma rikici a birnin Kaduna.

Daga bisani Gwamna Elrufai ya halarci wurin domin ganin matafiya basu fuskanci wata matsala ba.

Ranar Asabar, gwamman ya ce zai tashi garin na Gonin Gora dungurungun idan matasan garin suka ci gaba da tare mutane suna kashe su.

Da yake jawabi a filin "Hannu a Yawa" na gidan rediyon tarayya na Kaduna, Gwamna Elrufai ya ce "ina ba mutanen Gonin Gora shawara cewa wannan abin da matasansu suke yi su daina idan ba haka ba wallahi tallahi zan tashi garin."

"Ba za mu yarda su rika rufe hanya su hana mutane shiga ko fita daga gari suna kashe su ba. Za mu sa jami'an tsaro su rika duba wurin amma idan ba su daina ba, garin da kan shi bai fi karfin gwamnati ba."

Gwamnan na Kaduna ya yi wannan jawabi ne daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ce 'yan sanda sun cafke mutum 32 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar.