Fitaccen dan siyasar Nigeria Tony Anenih ya rasu

Tony Anenih

Asalin hoton, Daily Post Nigeria

A ranar Lahadi ne tsohon ministan ayyuka da gidaje Tony Anenih ya rasu.

Majiyoyi da dama dai sun tabbatar da mutuwar tsohon ministan ciki har da dansa.

Mr Anenih, ya rasu yana da kimanin shekara 85 a duniya a wani asibiti da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya bayan ya sha fama da cutar da ba a bayyana ba.

An dai haifi Mr Anenih ne a jihar Edo, kuma yana daga cikin masu fada aji a cikin siyasar Najeriya, inda a dalilin haka ne ake kiransa da suna Mr Fix.

Tony Anenih ya rike mukamai da dama a jam'iyyun siyasar Najeriya, ciki har da shugaban jam'iyyar NPN a jiharsa a shekarar 1981 zuwa 1983, inda har ake ganin ya taka muhimmiyar rawa a zaben 1983 mai cike da ce-ce-ku-ce a jiharsa ta Bendel a wancan lokaci inda ya taimaka wa Samuel Ogbemudia ya samu nasara.

Kazalika mr Anenih, ya rike mukamin shugaban jam'iyyar SDP na kasa a 1993.

Fitaccen dan siyasar ya kasance daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP, inda a nan ne har shugaba Olusegun Obasanjo ya bashi mukamin ministan ayyuka.

Asalin hoton, Information Nigeria

Baya ga haka ya kasance daga cikin 'yan kwamitin amintattu na jam'iyyar ta PDP.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da al'ummar jihar Edo da kuma jam'iyyar PDP.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, ta ce an yi rashin babban jigo wajen hada kan 'yan kasa a Najeriya.

Shima dan takarar shugabancin Najeriyar a karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce mutuwar daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyarsu babban rashi ne, kuma ba za a taba mantawa da irin gudunmuwar da bayar ga jam'iyyar ba.

Kazalika jam'iyyar ta PDP ma ta bayyana alhininta bisa ga rashin da suka yi, inda a cikin shafinta na twitter ta ce, ta kadu matuka bayan samun labarin rasuwar Tony Anenih.

Asalin hoton, tell.ng

Tony Anenih, ya mutu ya bar mace da kuma da daya.