An tabbatar da mutuwar mai Leicester City a hadarin jirgi

Mr Vichai

An tabbatar da mutuwar mai kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a hadarin da jirginsa ya yi a wajen fillin wasan kungiyar.

Mista Vichai Srivaddhanaprabha, da wasu ma'aikata biyu da matukin jirgin da kuma fasinja guda ne suka mutu bayan jirgin ya fado jim kadan da barinsu fillin wasa da aka buga wasan Premier a daren ranar Asabar.

Shaidu sun ce jirgin mai saukan ungulu ya yi ta watangariri a sama kafin daga bisani ya fado da karfi inda hayaki ya turnuke ko ina.

Dubban mutane ne su ka yi dafifi inda suka ajiye furannin da kyallaye domin nuna alhini a kan abinda ya faru.

Mr Vicahi, ya mutu yana da kimanin shekara 60 a duniya, inda kuma ya bar mace guda da 'ya'ya hudu.

Ya sayi kungiyar ta Leicester City ne a 2010, kuma a karkashinsa ne kungiyar ta lashe gasar Premier a 2016.

Kungiyar Leicester, ta bayyana Mr Vichai a matsayin mutumin kirki wanda ya ke matukar kula da iyalinsa.

Kungiyar ta ce ' A karkashin jagorancinsa, gabaki dayan 'yan kungiyar kan mu a hade yake ba bu wani bambanci a tsakaninmu, don haka wannan mutuwa ta sa babban rashi ne a gare mu da ma magoya bayanmu'.

Za a bude littafin rubuta ta'aziyya a filin wasa na King Power daga ranar Talata.

Karanta wasu karin labaran