Angela Merkel 'ba za ta sake tsayawa takara ba'

German Chancellor Merkel, 26 October 2018

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mrs Merkel ta kwashe shekara 18 tana shugabancin CDU

Wasu majiyoyi sun ambato Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tana gaya wa jam'iyyarta ta CDU cewa ba za ta ake tsayawa takarar shugabancinta a watan Disamba ba.

Ta dauki matakin ne bayan jam'iyyar ta sha mummunan kaye a zabukan larduna lamarin da ke barazana ga ci gaba da zamanta a matsayin gamayyar jam'iyyu da ke mulki.

Tun shekaar 2000 Mrs Merkel ke shugabancin jam'iyyar CDU, abin da ya sa ta zama daya daga cikin shugabanninta masu karfin fada a ji.

Ta zama Shugabar Gwamnatin Jamus a 2005 - kuma tana son ci gaba da kasancewa a kan mukamin.

Rahotanni sun ambato Mrs Merkel tana shaida wa manyan jami'an jam'iyyar CDU cewa za ta sauka daga shugabancinta bayan jam'iyyar da ke da ra'ayin rikau ta SPD ta yi nasara a zaben da aka gudanar a jihar Hesse a karshen makon jiya.

Amma kafofin watsa labaran kasar sun ambato ta tana cewa za ta ci gaba da kasancewa a matsayin Shugabar Gwamnati.

Hakan dai ya yi karo da matsayinta na baya inda ta ce shugabancin jam'iyya da shugabancin gwamnatin Jamus suna tafiya kafada da kafada.