An kwantar da shugaban kasar Gabon a asibiti

Ali Bongo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ali Bongo yana fama da cutar matukar gajiya

An kwantar da shugaban kasar Gabon Ali Bongo a asibiti inda yake fama da cutar matukar gajiya ko da yake mai magana da yawunsa ya ce yana samun sauki.

Shugaba Bongo ya soma rashin lafiyar ne lokacin da ya kai ziyara Saudiyya makon jiya kuma yanzu haka yana can kwance a asibiti.

Mai magana da yawunsa Ike Ngouoni ya ce ya yi matukar gajiya saboda ayyukan da ya yi a watannin da suka gabata.

Ya yi kira ga 'yan kasar ta Gabon su sanya ido kan labaran kanzon-kurege da ake watsawa game da shugaban nasu a shafukan sada zumunta, yana mai cewa fadar shugaban kasa za ta rika shaida musu halin da yake ciki a kai-a kai.

Mr Bongo, mai shekara 59, ya zama shugaban kasa bayan mutuar mahaifinsa Omar Bongo a 2009.

Omar Bongo ya zama shugaban kasa a 1967.