An 'kama' minista yana wasa da al'aurarsa

Malusi Gigaba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da aka dauki bidiyon Malusi Gigaba ba

An zargi jami'an tsaron Afirka ta Kudu bisa yin kutse a cikin wayar wani dan siyasa bayan wani bidiyon da ke nuna shi yana yin wasa da al'aurarsa ya bayyana.

An yada bidiyon mai tsawon dakika 13 da ya nuna ministan cikin gida Malusi Gigaba yana wasa da al'aurarsa a shafukan sada zumunta.

Mai magana da yawun ministan ya zargi jami'an tsaro da yin kutse cikin wayarsa suka sace bidoyin sannan ya zargi wani dan siyasa dan adawa da rarraba shi.

Ya kara da cewa a bara ne ministan ya rika samun sakonnin da ke yi masa barazana.

Ranar Lahadi Mr Gigaba ya wallafa sakonni a shafinsa na Twitter inda ya nemi gafarar iyalinsa bisa abin da ya yi.

Wakilin BBC a Afirka ta Kudu Milton Nkosi, ya ruwaito cewa an rarraba bidiyon sosai a manhajar WhatsApp tsakanin 'yan kasar.

Mr Gigaba ya ce ya ki bayar da kudi ga mutanen da suke son damfararsa game da batun.

Mai magana da yawunsa, Vuyo Mkhize, ya shaida wa kafar watsa labarai ta SABC cewa 'yan damfarar sun nemi ministan ya ba su $690,000.

"Jami'an tsaro ne suka yi kutse cikin wayar ministan inda suka saci bidiyon," in ji shi.