An kama mutum 93 kan rikicin Kaduna

Sufeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris

Asalin hoton, FACEBOOK NPF

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kama akalla mutum 93 wadanda ake zargi da hannu a rikicin da ya barke a jihar Kaduna.

Rikicin, wanda aka soma daga garin Kasuwar Magani mako biyu da suka wuce, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan kasar Mr Jimoh Moshood ya aike wa manema labarai ranar Litinin ta ce ana binciken 43 daga cikin mutanen da kama yayin da 'yan sanda ke tsare da mutum 50 kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

Mr Moshood ya ce an tsananta bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi da hannu a rikicin wadanda suka tsere.

A cewar sanarwar, "Yanzu zaman lafiya ya dawo a dukkan sassan jihar Kaduna, musamman a garin Kasuwar Magani da kuma kudancin Kaduna."

Rikicin na jihar Kaduna ya tilasta wa hukumomi sanya dokar hana fita a birnin Kaduna da wasu sassan jihar.

Sai dai a sanarwar da kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi ya ce an sake sassauta dokar hana zirga-zirga a birnin Kaduna da kewayensa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewarsa, "Ranar Lahadi mazauna birnin za su iya yin zirga-zirga har zuwa karfe biyar na yamma. Daga Litinin, 29 ga watan Oktoba, mutane za su iya zirga-zirga daga shida na safe zuwa biyar na yamma.

"Ana sa ran kasuwanni da bankuna za su bude. Amma za a ci gaba da tsaurara dokar hana zirga-zirga da daddare," in ji sanarwar.

A karshen makon jiya ne aka sake sanya dokar hana zirga-zirgar a birnin na Kaduna da kewaye da kuma wasu yankunan karamar hukumar Kachia bayan kisan da aka yi waani basaraken da masu satar mutane suka sace.

Mutane da dama ne dai suka mutu tun daga makon jiya sanadiyar rikicin da aka yi a garin Kasuwan Magani da ke kudancin jihar.

Ko da a ranar Juma'a sai da wasu matasa a garin Gonin Gora da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka toshe hanya da zummar far ma matafiya.

Sai dai jami'an tsaro sun tarwatsa su.

Za a tashi Gonin Gora

Matasan garin sun sha tare matafiya suna kashe su da zarar an soma rikici a birnin Kaduna.

Daga bisani Gwamna Elrufai ya halarci wurin domin ganin matafiya basu fuskanci wata matsala ba.

Ranar Asabar, gwamman ya ce zai tashi garin na Gonin Gora dungurungun idan matasan garin suka ci gaba da tare mutane suna kashe su.

Da yake jawabi a filin "Hannu a Yawa" na gidan rediyon tarayya na Kaduna, Gwamna Elrufai ya ce "ina ba mutanen Gonin Gora shawara cewa wannan abin da matasansu suke yi su daina idan ba haka ba wallahi tallahi zan tashi garin."

"Ba za mu yarda su rika rufe hanya su hana mutane shiga ko fita daga gari suna kashe su ba. Za mu sa jami'an tsaro su rika duba wurin amma idan ba su daina ba, garin da kan shi bai fi karfin gwamnati ba."

Gwamnan na Kaduna ya yi wannan jawabi ne daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ce 'yan sanda sun cafke mutum 32 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar.

Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna