Lion Air: Me zai sa sabon jirgin sama ya fado?

Artists impression of a Boeing 737 Max 8 plane

Asalin hoton, Boeing

Bayanan hoto,

Jirgin samfurin MAX 8 sabo ne, kuma bai wuce watanni da aka fara aiki da shi ba

Wani jirgin sama mallakin kamfanin Lion Air ya fada cikin teku dauke da kusan mutum 190 a cikinsa kim kadan bayan ya tashi daga Jakarta, babban birnin Indonisiya.

An dai mayar da hankula kan cewa jirgin, wanda samfurin Boeing 737 MAX 8 ne sabo fil ne. Wannan ne karo na farko da irin wannan hatsari ya rutsa da irin wannan jirgin.

Kawo yanzu dai ba a sami cikakken bayani game da hatsarin, kuma sai an gudanar bincike kafin a iya sanin dalilin aukuwarsa.

Yawancin hatsarin jirgin sama na aukuwa ne a dalilin abubuwa biyu, na farko laifin na'ura, na biyu kuma kuskuren dan adam.

To ko akwai wani abu da za a iya tsinta cewa jirgin sabo fil ne?

An dai fara amfani da jirgin mai samfurin Boeing 737 MAX 8 a sheakarar da ta gabata ne.

A baya kamfanin Lion Air ya sanar cewa yana alfahari cewa shi ne kamfanin da ya fara amfani da jirgin a kasar Indonisiya, kuma har ya yi odar guda 218.

Shi wannan jirgin da ya yi hatsari sabo ne, domin a watan Agusta aka fara amfani da shi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito shugaban kamfanin Lion Air na cewa jirgin ya sami wata matsalar na'ura da aba a fayyace ta ba a tafiyar da yayi kafin wannan.

Amma ya ce an warware matsalar kamar yadda tsarin aiki ya tanada.

Shugaban Lion Air Edward Sirait ya kuma ce kamfanin na da jiragen sama guda 11 dukkansu kuma samfurin Boeing 737 Max ne, kuma ya ce ba su da niyyar daina amfani da sauran jiragen.

Mista Ostrower editan mujallar sufurin jiragen sama ne, ya ce da alama tangardar na'ura ce ta janyo hatsarin:

"Ban san abin da zai iya janyo sabon jirgi kamar wannan ya yi hatsari irin wannan ba, domin akwai abubuwa da dama da ka iya zama sanadiyyar hatsari irin wannan."

Mista Ostrower ya kuma ce a tarihi, jirgin samfurin Boeing 737 MAX na da farin jini matuka, domin an fi sayensa fiye da sauran jiragen sama.

Kawo yanzu kamfanoni sun yi odar irinsa guda 4,700.

Kamfanoni kamar American Airlines da United Airlines da Norwegian da FlyDubai na cikin wadanda suka yi odar jirgin.