Sojoji sun sake yin artabu da 'yan Shi'a a Abuja

Wasu daga cikin 'yan Shi'a da rikicin ya rutsa da su

Asalin hoton, Ibrahim Musa

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan Shi'a da rikicin ya rutsa da su

'Yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta 'yan Shi'a sun sake yin artabu da sojoji a unguwar Maraba da ke kusa da Abuja, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Rikicin ya fara ne a lokacin da 'yan Shi'ar suke wani tattaki daga cikin jihar Nasarawa zuwa cikin birnin na Abuja, a cewar rahotannin.

Wasu da suka gane ma idanunsu lamarin sun ce sojojin sun "hana 'yan Shi'ar shigewa, kuma sun umarce su da su koma inda suka fito."

Sai dai duk kokarin ji ta bakin jami'an tsaron kasar ya ci tura don ba su amsa kirar wayar da muka yi musu ba.

Don haka babu tabbaci kan mutanen da suka mutu ko jikkata sanadiyyar rikicin.

Asalin hoton, Ibrahim Musa

Bayanan hoto,

Kimanin shekara uku ke nan da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da tsare jagoran 'yan Shi'an Sheikh Ibrahim Zakzaky

Wani mazaunin unguwar ta Maraba, Friday ya shaida wa BBC cewa rikicin ya auku ne a daidai wata mahadar motoci mai suna Kugbo Junction a unguwar Maraba da ke jihar Nasarawa.

Ya kuma ce bayan da 'yan Shi'an suka ci gaba da nufo wurin da sojojin suka ja daga ne rikicin ya barke.

Wani ma'aikacin BBC, Ahmed Wakili Zaria, wanda yake unguwar lokacin da abin ya faru, ya ce sojojin sun fara yin harbi a iska ne kafin daga baya suka rika harbin 'yan Shia'ar saboda sun ki janyewa kamar yadda aka umarce su.

" 'Yan Shi'an sun taru daidai unguwar Maraba, suna kokarin wuce wa cikin birnin Abuja, sojojin Najeriya kuma sun bude masu wuta,"in ji shi.

Ya kuma ce "Na ga gawarwaki 11 a wurin da aka yi wannan rikicin, har ma da gawar wata mata wadda ta mutu amma dan da take goye da shi ke ta kuka".

Mun tambayi Ibrahim Musa, wanda shi ne kakakin kungiyar ta 'yan uwa Musulmi abin da ya sani game da wannan rikicin.

"Mun fara muzahararmu daga Maraba Bus Stop daidai karfe 12, to daidai misalin karfe 4 mun isa wani junction na sojoji, to a nan ne suka bude man wuta kuma alal hakika sun kashe mutane da yawa," in ji shi.

An samu irin wannan rikicin tsakanin mabiya kungiyar 'yan uwa Musulmin da sojoji a garin Zuba da ke yankin Abuja a karshen mako.

A halin da ake ciki, mutane sun kauracewa yankin, kuma an rufe dukkan kasuwanni da ofisoshi da shagunan da ke kusa da wurin saboda rikicin.

Jami'an tsaro sun rufe dukkan hanyoyin shiga da fita Abuja daga wannan yanki, kamar yadda mazauna yankunan suka bayana wa BBC.