Bidiyon da ke nuna wasu sassan jirgin da ya fadi a teku a Indonesia

Bidiyon da ke nuna wasu sassan jirgin da ya fadi a teku a Indonesia

Wani jirgin sama kirar Boeing 737 na kamfanin sufurin jiragen sama na Lion Air dauke da mutane 189 ya fadi a teku jim kadan bayan ya tashi daga Jakarta, babban birnin Indonesia.

Wani babban jami'i a Hukumar kare afkuwar bala'i ta kasar, Sutopo Purwo Nugroho ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter, wanda ake tunanin yana nuna baraguzan jirgin da aka gano a teku.

An kuma gano wasu kayan da ake tunanin na mutanen da ke cikin jirgin ne.