Malaria: Yadda karnuka za su taimaka wajen kawar da cutar

  • Daga James Gallagher
  • Wakilin BBC a bangaren lafiya da kimiyya
Sniffer dog

Asalin hoton, Once Upon a Pixel

Bayanan hoto,

Dabbobin na gane wani nau'i na kamshi ta hanyar amfani da kayan mutane masu dauke da cutar

Masana kimiyya a kasashen Birtaniya da Gambiya sun ce sun gano hujja ta farko wacce ke nuna cewa karnuka na iya shinshino cutar Malaria.

Sun horar da karnuka su rika gane kamshin kayan mutanen da ke dauke da cutar.

Ana fatan yin amfani da dabbobin don dakatar da yaduwar cutar Malaria da kuma taimakawa wajen kawar da cutar.

Ko da yake, har yanzu binciken yana matakin farko, kwarraru sun ce binciken zai iya haifar da sababbin hanyoyi na gwajin cutar.

Bincike ya riga ya nuna cewa kanshin jikin masu cutar Malaria yakan sauya, inda yake daukar hankalin sauro masu yada cutar.

Safa mai wari

An aika safar da ta kwana a kafar yara da ke yankin Upper River Region a Gambia, a Afirka ta Yamma, zuwa Birtaniya.

30 cikin 175 safannin na yaran da su ke dauke da cutar ne. Cikin safar 175 da aka tura Birtaniya, guda 30 wacce yara masu dauke da kwayar cutar Malaria su ka sa ce.

Safar mai warin gaske ta isa Cibiyar kula da Karnuka masu Sunsuna da ke Milton Keynes.

Dama dai karnukan da ke cibiyar sun kware wajen shinshino ciwon daji da cutar Parkinson's.

Don haka da a ka zo kan batun gano malaria, sakamakon da aka gabatar a taron shekara-shekara na Hukumar nazari kan cututtukan yankuna masu zafi da ke Amurka, ya nuna cewa karnuka zasu iya gano samfuri bakwai cikin samfurori 10 daga yaran masu cutar.

Asalin hoton, LSHTM

Bayanan hoto,

An aika safar da ta kwana a kafar yara da ke yankin Upper River Region a Gambia, a Afirka ta Yamma, zuwa Birtaniya

Amma kuma sun yi kuskuren wajen gane cewa cikin yara 10 masu lafiya, daya na fama da cutar malaria.

Jagoran masu binciken Farfesa Steve Lindsay, na Jami'ar Durham, ya ce ya yi "matukar murna" game da sakamakon binciken da aka samu, amma da sauran lokaci kafin a fara amfani da karnuka sosai wajen gano cutar.

Har ila yau, masu bincike suna bukatar inganta gwajin karnukan ta yadda za'a iya gwada su akan mutane maimakon safa, sannan a bincika a gani ko dabbobin zasu iya shishino mabambantan nau'i na malaria.

Manufar ita ce wata rana a iya amfani da karnukan da aka horar da su musamman a filayen jirgin sama don hana yaduwar cutar.

Karnuka zasu iya auna al'umma guda a cikin kankanin lokaci.

Sun yi wa kimiyya fintinkau

Dr Chelci Squires, na makarantar kula da lafiya da nazari kan cututtukan yankuna masu zafi da ke London, ya shaida wa BBC cewa: "karnuka sune ainihin masu sunsuna, saboda haka ya na da kyau mu ajiye su."

"Sun fi sauran hanyoyin gwaji sauri wadanda su kan dauki minti 20 kuma suna bukatar kulawar kwarrare.

Ana bukatan sabbabin na'urori gwaji da magance malaria.

A cewar wani rahoto da aka gudanar a kan cutar, lamarin ya karu da miliyan biyar zuwa miliyan 216 a kowace shekara.

Binciken hadin gwiwa ne tsakanin Cibiyar Kula da Cutar Malaria ta Gambia; Cibiyar Nazarin Lafiya ta Gambia; Hukumar Kula da Karnukan masu Sunsuna; Jami'ar Durham; Makarantar kula da Lafiya da Nazarin cututtukan yankuna masu zafi da ke Landan da Jami'ar Dundee.