Ko taron dangin PDP zai iya kada Buhari?

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Asalin hoton, PDP

A Najeriya, babbar jam'iyyar adawar kasar PDP, ta ce ta na ci gaba da tattaunawa da wasu kananan jam'iyyu na kasar don tsayar da dan takarar shugaban kasa guda da zai kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

A makon da ya gabata ne dai hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta fitar da alkaluman da ke nuna cewa 'yan takara 79 ne za su yi takarar mukamin shugaban kasa karkashin jam'iyyun siyasar kasar.

Shugaban kwamitin amintattu na Jam'iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, ya shaida wa BBC cewa, yawan 'yan takarar shugaban kasar bai firgita su ba.

Sanatan ya ce ai akwai jam'iyyu da kuma 'yan rakiyar jam'iyyu, don haka jam'iyyarsu ko kadan ba ta da wata fargaba a kan yawan masu neman kujerar shugaban kasa.

Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar ta PDP, ya ce suna da kwamiti na hadin kai na jam'iyyu kusan 35 wanda suka yarda cewa idan aka fito da mutum guda dukkansu za su bada goyon baya.

Sanata Walid ya ce, ' Muna nan muna tattauna wa da wadannan jam'iyyu domin su dawo samun maslaha a kan mutum guda da za a tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa'.

Sanatan ya ce, ya kamata 'yan Najeriya su tambayi kansu da kansu a kan ko jam'iyyar APC ta cika alkawuran da ta dauka?

Don haka su a yanzu suna masu jiran zabe ne na 2019 domin su samu nasara inji Sanata Walid.

Karanta wasu karin labaran