Mun kashe ‘yan Shi'a a Abuja — Sojin Nigeria

Sojin sun ce 'yan Shia sun far ma dakarunsu

Asalin hoton, Facebook/ HQ Nigerian Army

Bayanan hoto,

Sojin sun ce 'yan Shia sun far ma dakarunsu

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile harin da mabiya mazahabar Shia suka kai wa jami'anta a Abuja lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan Shia uku.

Ranar Litinin ne dai aka yi arangama tsakanin mabiya Shia da jami'an sojin a kan hanyar shiga Abuja, babban birnin kasar.

Wata sanarwa da rundunar sojin kasa ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce 'yan Shia sun far ma dakarunta da ke sanya ido a wuraren binciken ababen hawa da ke gadar Kugbo/Karu da misalin karfe uku na rana.

"Mabiya mazahabar wadanda ke da matukar yawa sun kutsa kai ta shingen binciken ababen hawa inda suka turmushe 'yan sanda. Daga nan ne 'yan sandan suka janye inda suka shiga cikin sojojin da ke yunkurin dakile harbe-harben da mutanen ke yi," in ji sanarwar.

Ta kara da cewa "lokacin arangamar ne mabiya mazahabar uku suka mutu san nan soji hudu suka jikkata, inda aka tura su asibiti domin karbar magani."

Rundunar sojin ta Najeriya ta ce tuni al'amura suka lafa a hanyar kuma kowa ya shiga harkokinsa kamar yadda aka saba.

Sai dai ta sha alwashin murkushe duk wata kungiya da ke da jimirin tayar da rikici.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Yadda aka soma rikicin

Rikicin ya fara ne a lokacin da 'yan Shi'ar suke wani tattaki daga cikin jihar Nasarawa zuwa birnin na Abuja, a cewar rahotannin.

Wasu da suka gane ma idanunsu lamarin sun ce sojojin sun "hana 'yan Shi'ar shigewa, kuma sun umarce su da su koma inda suka fito."

Wani mazaunin unguwar ta Maraba, Friday ya shaida wa BBC cewa rikicin ya auku ne a daidai wata mahadar motoci mai suna Kugbo Junction a unguwar Maraba da ke jihar Nasarawa.

Ya kuma ce bayan da 'yan Shi'an suka ci gaba da nufo wurin da sojojin suka ja daga ne rikicin ya barke.

Wani ma'aikacin BBC, Ahmed Wakili Zaria, wanda yake unguwar lokacin da abin ya faru, ya ce sojojin sun fara yin harbi a iska ne kafin daga baya suka rika harbin 'yan Shia'ar saboda sun ki janyewa kamar yadda aka umarce su.

" 'Yan Shi'an sun taru daidai unguwar Maraba, suna kokarin wuce wa cikin birnin Abuja, sojojin Najeriya kuma sun bude masu wuta,"in ji shi.

Ya kuma ce "Na ga gawarwaki 11 a wurin da aka yi wannan rikicin, har ma da gawar wata mata wadda ta mutu amma dan da take goye da shi ke ta kuka".

Mun tambayi Ibrahim Musa, wanda shi ne kakakin kungiyar ta 'yan uwa Musulmi abin da ya sani game da wannan rikicin.

"Mun fara muzahararmu daga Maraba Bus Stop daidai karfe 12, to daidai misalin karfe 4 mun isa wani junction na sojoji, to a nan ne suka bude man wuta kuma alal hakika sun kashe mutane da yawa," in ji shi.

An samu irin wannan rikicin tsakanin mabiya kungiyar 'yan uwa Musulmin da sojoji a garin Zuba da ke yankin Abuja a karshen mako.

A halin da ake ciki, mutane sun kauracewa yankin, kuma an rufe dukkan kasuwanni da ofisoshi da shagunan da ke kusa da wurin saboda rikicin.

Jami'an tsaro sun rufe dukkan hanyoyin shiga da fita Abuja daga wannan yanki, kamar yadda mazauna yankunan suka bayana wa BBC.