Ashe maza na kamuwa da sankarar mama?

  • Daga Ashley Lime
  • BBC Afirka, Nairobi

Moses Musonga bai taba tsammanin maza na iya kamuwa da cutar sankarar mama ba sai lokacin da aka yi masa gwaji inda aka ano yana dauke da cutar.

Mutumin mai shekara 67 dan kasar Kenya ya shaida wa BBC cewa ya yi matukar girgiza lokacin da likitoci suka shaida masa cewa yana dauke da mataki na uku na cutar daji a shekarar 2013, lamarin da ya jefa shi cikin matsanancin halin rayuwa.

"Ban yarda cewa ina dauke da cutar ba. Hasalima na yi matukar mamaki, saboda ban san akwai alaka tsakanin namiji da cutar sankarar mama ba, shi ya sa nake ganin me zai sa a ce ni kadai cikin miliyoyin maza ne ke dauke da cutar," in ji Mr Musonga.

Lamarin ya soma ne lokacin da ya ga wani kumburi maras zafi a kan mamansa na dama wanda ya rika girma a hankali.

Sai kuma kuma maman ya rika fitar da wani ruw mai doyi sannan ya rika jin zafi kirjinsa.

Lokitoci sun rika bai wa Mr Musonga, mai 'ya'ya biyar, maganin kashe radadi domin magance wannan cuta da basu an ko mece ce ba.

Ko da yake mamansa suna da girma fiye da na sauran maza, Mr Musonga bai taba yin tunanin wani abu ne da zai damu da shi ba.

Ya nemi taimako daga wurin msu bayar da magani lokacin da fatar da ke kan mamansa na dama ya fara zama gyambo.

Gwaje-gwajen da aka yi a kan fatar jikinsa sun tabbatar da cewa Mr Musonga yana fama da cutar sankarar mama.

"Ban san cewa sankarar mama ka iya shafar maza ba don haka ban lura cewa ina dauke da ita ba," in ji shi.

Dr Sitna Mwanzi, wata kwarariyar likitar sankara a asibitin da ke jami'ar Aga Khan ta birnin Nairobi, ta ce ba safai ake samun maza dauke da cutar daji ta mama ba.

Ta ce a duk mutum 100 da ke dauke da cutar sankarar mama, ana samun namiji daya ne kawai.

Me ya sa maza ke kamuwa da sankarar mama?

Ba a san takamaiman abin da ke sa maza ke kamuwa da sankarar mama ba amma dai hadarin kamuwa da ita yana karuwa ne saboda:

  • Kayoyin halitta da tarihin iyali ko dangi, ciki har da gadon gurbatattun kwayoyin halitta rukunin BRCA1 ko BRCA2
  • Yanayin da zai sa a samu karuwar sinadarin oestrogen a cikin jiki, ciki har da teba da larurar hanta
  • Idan an taba yin amfani da makamashi wajen daukar hoton bangaren kirjin mutum (radiotheraphy)

Babu tabbas kan ko za a iya daukar wasu matakai na rage kasadar kamuwa da cutar, sai dai wata kila daukar wadannan matakai zai iya taimakawa:

  • Cin abinci mai gina jiki
  • Motsa jiki idan mutum yana da teba
  • Kauracewa shan barasa da yawa

An samu wannan bayani ne daga: Hukumar lafiya ta Burtaniya

Za a yi gwaji kan kusan mutum 6,000 da ke fama da sankarar mama a Kenya a wannan shekarar, lamarin da zai sa su zama kashi 12.5 ciki 100 na yawan masu fama da cutar a kasar, a cewar wata kididdiga ta Globocan 2008, wacce ke aiki da Hukumar lafiya Ta duniya kan sankarar mama.

Ana sa ran za a samu mutum 170,000 da ke dauke da cutar a fadin Afirka a bana.

Dr Mwanzi ta ce maza sun fi fama da hadarin kamuwa da cutar sankarar mama saboda dalilai da dama, ciki har da kasancewa sun fi maza yawan sinadarin oestrogen a jiki.

"Idan kana da sinadarin oestrogen da yawa, zai haifar da wasu tsokoki wadanda daga bisani za su iya haifar da sankara," in ji ta.

Bayanan hoto,

Dr Mwanzi ta ce maza basu kai mata hadarin kamuwa da sankara ba

Dr Mwanzi ta kara da cewa akwai bukatar maza da mata su sanya ido sosai kan alamomin cutar, musamman kumburin mama.

Sauran alamomin cutar su ne sauyin sauyi a kan fatar da ke kan mama, fitar da ruwa mai dauke da jini daga kan mama da kuma sauye-sauyen da kuma girman mama.

Ta kara da cewa sankara kan sa mutum ya rame.

Dr Mwanzi ta ce babbar hanyar magance sankarar mama ita ce gashi ko kona ta da na'ura, ko yin tiyata ko kuma cire kwayoyin halittar da ke haddasa ta.

"Ya kamata maza su rika duba mamansu a kai-a kai domin ganin ko suna kumbura," in ji ta.