An kama wani yaro da ya yi shigar mata ya je jarrabawa

Dalibin ya sanya kayan makarantar 'yan mata

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Dalibin ya sanya kayan makarantar 'yan mata

An kama wani makadi mai azanci da ya yi shigar mata yayin wata jarrabawa a wata makarantar sakandire a Kenya.

Ya sanya kayan makarantar 'yan mata kuma ya ja hankalin sauran dalibai a lokacin da yake kida cike da fasaha, sabanin sauran daliban, a cewar jaridar Daily Nation ta kasar.

Ba a bayyana sunan yaron ba.

Lamarin dai ya faru ne a makarantar sakandiren 'yan mata ta Mukuyu da ke lardin Kakamega a yammacin Kenya.

Makadin dai dalibi ne a lardin Uasin Gishu da ke makwaftaka da Kakamega.

An kama shugaban makarantar da malamin da ke koyar da kida a makarantar.