Gwamnoni sun amince su yi karin albashin Naira dubu 22 a Najeriya

Kungiyar Kwadago a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar kwadago ta ce sai Naira dubu 30 za a biya karamin ma'aikaci

Gwamnonin Najeriya sun amince da matakin yin karin albashi mafi kankanta ga ma'aikatan kasar daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 22 da dari biyar.

Gwamnonin sun amince da matakin karin albashin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja a jiya Talata bayan matsin lamba daga kungiyoyin kwadago.

Shugaban kungiyar gwamnonin, da ya jagoranci taron Gwamnan jihar Zamfara Abdul'ziz Yari Abubakar ya ce matsayar da suka cimma ba wai adadin kudin ba ne kawai suka yi la'akari da shi har da diba tsarin samun zarafin iya biyan albashin.

Sai dai kuma kungiyar kwadago a Najeriya ta kalubalanci matakin da gwamnonin suka dauka wanda ta ce ya saba wa yarjejeniyar da suka amince ta biyan Naira dubu 30 ga karamin ma'aikaci.

Kungiyar ta ce tana kan bakanta na shiga yajin aiki a ranar 6 ga watan Nuwamba matukar gwamnonin suka kasa amincewa da bukatunta.

Kwamared Nasir Kabir jami'ain tsare-tsare na gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya ya shaida wa BBC cewa za su tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani idan har gwamnati ba ta amince da bukatunsu ba.

Ya kuma ce sun riga sun shirya, tare da sanar da mambobinsu matakin da suke shirin aiwatarwa.

Karanta wasu karin labaran