Me ya sa 'yan kwadago suka yi fatali da karin albashi?

Kungiyar Kwadago a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar kwadago ta ce sai Naira dubu 30 za a biya karamin ma'aikaci

Kungiyar kwadagon Najeriya ta yi watsi da albashi mafi karanci da gwamnoni suka kara daga N18,000 zuwa N22,500.

Kungiyar ta ce ta dauki mataki ne saboda a alkawarin da suka yi da gwamnonin a baya sun ce N30,000 za su kara a matsayin albashi mafi karanci.

Ranar Talata gwamnonin suka amince da matakin karin albashin a wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja bayan matsin lamba daga kungiyoyin kwadago.

Shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan jihar Zamfara, Abdul'ziz Yari Abubakar ya ce ba adadin kudin kawai suka yi la'akari da shi ba har da duba tsarin samun zarafin iya biyan albashin.

Sai dai kuma kungiyar kwadago ta kalubalanci matakin da gwamnonin suka dauka wanda ta ce ya saba wa yarjejeniyar da suka amince ta biyan N30,000 ga karamin ma'aikaci.

Kungiyar ta ce tana kan bakanta na shiga yajin aiki a ranar 6 ga watan Nuwamba idan gwamnonin suka ki amincewa da bukatunta.

Jami'in tsare-tsare na gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya, Kwamared Nasir Kabir, ya shaida wa BBC cewa za su tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani idan har gwamnati ba ta amince da bukatunsu ba.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Gwamnonin sun ce sun yi la'akari da ikon iya biyan albashi

Ya kuma ce sun riga sun shirya, tare da sanar da mambobinsu matakin da suke shirin aiwatarwa.

Karanta wasu karin labaran