Ko basirar na'urori na iya taimaka wajen rage rikicin addini?

Religions graphic Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana gwajin wata manhajar da ke kwaikwayar halayyar dan Adam domin a ga ko za ta iya taimakawa wajen magance tashin hankali mai nasaba da addini.

Masu bincike na amfani da sabuwar fasahar zamani ta basirar na'urori "artificial intelligence" wajen kamanta abubuwan da kan janyo rikicin bangaranci.

Tsarinsu ya kunshi dubban kofin halayen mutane da ke wakiltar kabilu da jinsuna da addinan duniya.

Kasashen Norway da Slovakia na gwaje-gwajen sabuwar fasahar da zummar magance tashin hankalin da ke faruwa tsakanin 'yan ci-rani Musulmi da ke zama a kasashen da galibi na Kirista ne.

Masu binciken daga Jami'ar Oxford na fatan manhajar tasu za ta taimaka wa gwamnatoci wajen magance matsaloli kamar harin ta'addanci da ya auku a birnin Landan.

Amma wani masani mai zaman kansa ya ce manhajar na bukatar a kara gudanar da bincike a kanta kafin a fara amfani da ita a zahirance.

Farfesa Noel Sharkey: "Wannan manhajar na iya zama mai muhimmanci wajen gudanar da bincike bayan an kammala aiki a kanta".

Asalin mutane salihai ne

An wallafa sakamakon binciken ne a wata mujallar bincike, mai suna Journal of Artificial Societies and Social Simulation, kuma ta bayyana cewa asalin mutane masu son zaman lafiya ne.

Kuma ko a lokutan tashe-tashen hankali kamar girgizar kasa, wadannan mutum-mutumin na manhaja na zaman lafiya tsakaninsu.

Amma a wasu lokutan, manhajar ta nuna cewa wasu mutane na goyon bayan tashin hankali.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Masu binciken sun jawo hankali kan rikicin yankin Arewacin Ireland wajen tsara yanayin manhajar

Masu binciken sun jawo hankali kan rikicin yankin Arewacin Ireland wajen tsara yanayin da masu binciken ke kira "tashin hankali irin na nuna bambancin launin fata".

Rikicin wanda ya hada da na siyasa da na al'adu ban da na addini ya lakume rayukan mutum 3,500 a cikin shekaru 30 da aka shafe an yinsa.

Ba a gadon tsattsauran ra'ayi

Tsarin basirar na'urori mai kwakwalwa da aka yi amfani da shi wajen hada manhajar ya hada da tarzomar Gujarat ta 2002 a Indiya.

Mutum dubu biyu ne suka rasa rayukansu a wannan rikicin da aka yi tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmai.

Daya daga cikin masu binciken, Justin Lane ya ce: "Yin amfani da wannan sabuwar fasahar wajen nazarin addinai da al'adu na bukatar mu lura da halayen dan Adam, saboda halayyarmu ita ce harsashin samar da addini da al'ada.

Bambanci a zuci ya ke

Masu binciken sun yi imanin cewa hanya daya da za ta rage tashin hankali irin na addini da ta'addanci shi ne a kirkiri yanayin da zai sauya yadda mutane ke kallon baki a matsayin abin tsoro.

Mista Lane ya ce "Muna rayuwarmu ne a cikin wani tsukakken yanayi da muke tace bayanan da ba namu ne ba."

"Da zarar an ce akwai yiwuwar wata matsala, sai kawai mutane su dauka lalle matsalar da gaske za ta auku."

Labarai masu alaka