Kun san inda aka gano gawarsa Janar Alkali a Jos?

  • Sani Aliyu
  • Multimedia Broadcast Journalist
The well where the body of late General Alkali was found

Asalin hoton, Ikechukwu Oha

Bayanan hoto,

Rijiyar da aka gano gawar marigayin

Rundunar sojojin Najeriya ta gano gawar Janar Idris Alkali mai ritaya a wata rijiya da ke Gushwet a gundumar Shen ta karamar hukumar Jos South a jihar Filato.

Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar, Birgediya Janar Umar Mohammed ne ya bayyana haka ga maneman labarai a ranar Laraba.

Janar Mohammed ya ce daya daga cikin wadanda suka mika kansu ga 'yan sanda ne ya nuna wa sojoji rijiyar, wadda "ba a amfani da ita."

Duk da cewa likitoci ba su gudanar da bincike a kan gawar ba, amma hukumomin sojoji sun tabbatar da cewa gawar da aka gano ta marigayin ce.

Yadda aka gano gawar

"Kamar yadda aka sani, mun sanar da bacewar Manjo Janar Idris Alkali ranar 3 ga watan Satumba."

Ya kara da cewa "Saboda haka ne muka bazama nemansa, kuma mun gano motarsa wadda a cikinta muka gano wasu daga cikin kayansa, kuma wannan ne ya bayyana mana cewa wani mummunan abu ya same shi."

"A makon jiya kuma mun gano wani kabarin da aka tone, wanda ya ta tabbatar mana da cewa an kai gawarsa wani wuri bayan an fara binne ta a wurin."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Hukumomin sojin kasar sun yi shelar neman wasu mutum 13 da suke da hujjar cewa suna da hannu wajen bacewar marigayin.

Mutanen sun hada da hakimin gundumar Du, Yakubu Rap da Pam Gyang Dung wanda direban motar bas ne da Timothy Chuan da kuma wasu masu aikin gyaran bodin mota Da Chuwang Samuel wanda aka fi sani da Morinho da Nyam Samuel wanda shi kuma aka fi sani da Soft Touch.

"Wasu daga cikin wadanda ake neman sun kai kansu ga 'yan sanda, a cikinsu ne wasu suka nuna mana wannan rijiyar, inda muka gano gawarsa", inji Janar Mohammed.

Kawo yanzu, rundunar sojojin Najeriya sun ce sun kammala bangarori biyu cikin uku da aka umarce su su yi.

Na farko shi ne an gano gawar marigayin. Na biyu kuma shi ne an gano motarsa, wato samfurin Toyota Corolla.

Janar Mohammed ya bayyana mataki na uku da ya rage a dauka.

"Abin da ya rage shi ne hukunta duk wadanda ke da hannu a wajen aikata wannan mummunan laifin, kuma duk wanda aka samu yana da hannu, komai girmansa sai ya fuskanci hukunci."

Asalin hoton, Ikechukwu Oha

Bayanan hoto,

Gawar marigayi Janar Idris Alkali bayan an fito da ita daga cikin rijiyar

Bacewar Janar Alkali

A ranar 29 ga watan Satumba ne rundunar cika aiki da babban hafsan sojin kasa ta Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya kafa don neman Janar Alkali, ta gano motarsa a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na karamar hukumar Jos Ta Kudu.

Ana zargin cewa an sace Janar Alkali ne wanda yake yin bulaguron a motarsa.

A wancan lokacin rundunar sojin Najeriya ta wallafa hoton motarsa a shafinta na Twitter.

Ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne kuma rundunar ta yi karin bayani kan abubuwan da ta gano sakamakon ci gaba da neman Janar Alkali da ake yi.

Baya ga mutum 30 da ta ce ta kama a yankin Du, ta kuma ce ta kama manyan bindigogin gargajiya uku da kananan bindigogi uku da wukake da takubba da adduna da rodi da babura biyar da katin shaidar kungiyar 'yan sa-kai da kuma takalma sau-ciki guda biyu.

Wane ne Janar Alkali?

  • Dan asalin jihar Yobe ne
  • Ya shafe shekara 35 yana aikin soja
  • Ya yi ritaya a watan Yunin 2018
  • Shi ne babban jami'in gudanarwa na rundunar sojin Najeriya kafin ya yi ritaya