Ma'aikatan Google na zaman dirshan kan neman hakkinsu

WALKOUT ORGANISERS

Asalin hoton, WALKOUT ORGANISERS

Ma'aikatan kamfanin Google a fadin duniya suna gudanar da wani zaman dirshan da ba su taba yin irinsu ba kan yadda kamfanin ke tafiyar da mata ma'aikata da kuma kananan kabilu.

Masu zaman dirshan din na son a yi wata hobbasa da za ta kawo karshen rashin daidaito a wajen biyan ma'aikata da bayar da damarmaki.

Shugaban Google Sundar Pichai, ya ce yana goyon bayan hakkokin ma'aikata na daukar mataki tare da alkawarin biya musu bukatunsu.

An dade ana kullatar juna ta karkashin kasa, sai dai tura ta kai bango ne bayan da aka gano cewa wani tsohon shugaban kamfanin Andy Rubin, ya karbi dala miliyan 90 a matsayin kudin sallamar barin aiki - duk da cewa Google ya amince akwai hujja mai karfi game da zargin da ake masa na lalata.

Asalin hoton, WALKOUT ORGANISERS

Asalin hoton, WALKOUT ORGANISERS

Asalin hoton, WALKOUT ORGANISERS

Asalin hoton, WALKOUT ORGANISERS

Sai dai ya musanta zargin.

Amma Mr Pichair ya amince cewa kamfanin ya kori mutum 48 a shekara biyun da suka gabata kan batun lalata.

Ma'aikatan Google na kuma neman a sauya yadda ake tunkarar zarge-zargen lalata a kamfanin, ciki har da kawo karshen yarjejeniyar da ke tilasta ma'aikatan masu korafi bayyana a gaban wani kwamitin shiga tsakani na cikin gida, lamarin da ka iya bai wa wadanda abin ya shafa dama su shigar da kara a kotu.

Ma'aikatan na wannan zama ne a biranen Zurich da London da Tokyo da Singapore da kuma Berlin.