Rikicin Boko Haram: An kashe mutum 15 a wani hari a Borno

Boko Haram attack on some Borno villages

Wasu mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutum 15 a warin hari da suka kai ranar Laraba a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kauyukan da wannan harin na kusa da birnin Maiduguri ne, birnin da shi ne fadar gwamnatin jihar Borno, kuma cibiyar da rundunar sojojin kasar da ke yaki da kungiyar ta Boko Haram take.

An shafe shekara 10 ana wannan rikicin a yankin arewa maso gabashin Najeriya da sassan Jamhuriyar Nijar da Kamaru.

Amma duk da matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka tun 2015 da shelar da ta yi cewa ta fatattaki kungiyar, har yanzu tana kai hare-hare a yankunan jihar, har da ma sauran wurare a yankin arewa maso gabashin kasar.

A kauyen Kofa, wani dan jarida mai aiki da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya kirga gawarwaki biyar da aka kona su a cikin gidajensu.

Wani mai unguwa a kauyen Dolori ya ce an kashe mutum daya a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin, kana mazauna garin Bulabrin sun sanar da cewa an kashe mutum tara a wani harin da aka kai garin.

Rundunar sojojin kasar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa an gano gawar wani mutum bayan da Boko Haram ta kai wani hari a kasuwar Dolori, inda suka cinna wa gine-gine wuta, amma sun tsere da sojojin Najeriya suka isa garin.