Meaza Ashenafi ta zama alkalin alkalan kotun koli Habasha

Meaza Ashenafi

Asalin hoton, ullstein bild

An nada Meaza Ashenafi wadda fitacciyar lauyar kasar Habasha ce mai rajin kare hakkin dan Adam a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci kotun kolin kasar.

Firai minista Abiy Ahmed ne ya mika sunanta ga majalisar kasar, wadda ta amince da nadin da gagarimin rinjaye.

Wannan nadin shi ne na baya-bayan nan a jerin nade-naden da mata ke samun manyan makamai a kasar.

A makon jiya ma Sahle-Work Zewde ta zama mace ta farko da aka nada a matsayin shugabar kasar, duk da cewa mukamin na jeka-na-yi-ka ne.

Makonni biyu da suka gabata kuma, Firai ministan ya nada ministocinsa, inda ya ba mata rabin mukaman.

Madam Meaza ce ta kafa Kungiyar Lauyoyi Mata ta Habasha a 1995, kuma kafin nan ta rike mukamin alkali a wata babbar kotu inda ta bayar da shawarwari wajen samar da sabon kundin tsarin mulkin kasar a shekarun 1990.

Ta taba yin aiki a hukumar da ke kula da batun tattalin arzikin nahiyar Afirka ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma ta bayar da gudunmawa wajen kafa bankin mata zalla na farko a kasar.

Tashar watsa labarai ta Fana Broadcasting Corporate (FBC) ta sanar da bikin rantsar da sabuwar alkalin a wani sakon Twitter da ta aika:

An dai taba nuna rayuwar Madam Meaza a fim din Difret da shararriyar 'yar fim din nan ta Hollywood, Angelina Jolie ta shirya.

Fim din ya nuna fafutukar da wata lauya ta yi wajen kare hakkin wata yarinyar da aka sace daga kauyensu kuma aka so a tilasta ma ta yin aure.