Rikicin 'yan Shi'a: Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta yi bincike

'Yan Shi'ar kuma sun bukaci a sako shugabansu a Najeriya Ibrahim El-Zakzaky da ke hannun gwamnati

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Shi'ar sun bukaci a sako shugabansu a Najeriya Ibrahim Zakzaky da ke hannun gwamnatin kasar

Kasar Amurka ta nemi gwamnatin Najeriya ta gudanar da cikakken bincike kan rikicin baya-bayan nan tsakanin 'yan Shi'a da sojoji tare da daukar matakin da ya dace na hukunta masu hannu wajen taka dokar kasar.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka a kasar ya fitar na cewa ya damu da kashe-kashen da aka samu sakamakon rikicin a wasu yankunan Abuja.

Ita dai kungiyar ta ce an kashe 'ya'yanta fiye da 50 a rikicin, amma rundunar sojin kasar ta ce 'yan Shi'a shida ne suka mutu.

Ofishin jakadancin Amurka ya kuma bukaci bangarorin biyu su kai zuciya nesa a arangamar da ta shafe tsawon kwanaki tsakanin mabiya babban malamin shi'ah, Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ke tsare a hannun hukumomi da kuma jami'an tsaron kasar.

Sai dai wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar Burgediya Janar John Agim ya shaida wa BBC cewa zargin ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, 'yan Shi'a ne suka far wa wani ayarin sojoji da ke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna don kai wasu kayan alburusai a yankin Zuba.

"Eh, adadin 'yan Shi'an da suka mutu, shida ne, kuma mu ma muna da sojojinmu da aka jikkata tsakanin ranar Lahadi da Litinin," in ji Janar Agim.

Ya ce a ranar Talata kuma mabiyan kungiyar sun shiga birnin Abuja, amma 'yan sanda ne suka tare su kuma daga labaran da ya samu an ce sun kama kimanin mutum 400.

A cewarsa 'yan sanda sun kama 'yan Shi'an ne "rike da makamai," ko da yake ya ce ba shi da cikakkun alkaluma na abin da ya faru ranar Talata.

Shi dai mai magana da yawun harka Islamiyya, Malam Abdullahi Usman ya yi ikirarin cewa adadin 'ya'yan kungiyar da suka mutu sakamakon arangamar zai iya karuwa.

Ya ce a yanzu haka an kashe mabiyan kungiyar 54, kuma yana fargaba game da makomar karin wasu da aka ji wa munanan raunuka.