Kashoggi abin tsoro ne - Yariman Saudiyya

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Saudiyya ta fada wa Amurka cewa Kashoggi dan kungiyar Brotherhood ne

Yariman Saudiya mai jiran gado Mohammed bin Salman ya shaida wa Amurka cewa dan jarida da aka kashe Jamal Kashoggi mutum ne mai hatsarin gaske,

Rahotanni sun ce Yarima Mohammed bin Salman ya fadi haka ne a wata tattaunawa da ya yi da fadar White House ta wayar tarho bayan ba a ji duriyar Kashoggi ba kafin Sadiyya ta amince da kisan dan jaridar.

Jaridar Washington Post ta ce an yi tattaunawar ne a ranar 9 ga watan Oktoba kuma Yarima Mohammed ya fada wa mai bai wa shugaban Amurka shawara kan sha'anin tsaro John Bolton cewa Kashoggi dan kungiyar 'yan uwa musulmi ne ta Brotherhood.

Kuma Yariman ya bukaci Fadar House ta mutunta dangantar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya.

Har yanzu ba a gano gawar dan jaridar ba, amma Turkiya da Amurka da Saudiyya dukkaninsu sun amince kashe shi aka yi a ofishin jekadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul a Turkiyya a ranar 2 ga Oktoba.

Amurka na nazarin takunkumi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Saudiyya na ci gaba da fuskantar matsin lamba

Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce suna bukatar lokaci domin samun kwararan sheda kan mutanen da ake zargi da aikata abin da ya kira mummunan laifi na kisan dan jarida Jamal Kashoggi.

A hira da wata kafar rediyo a St. Louis a Amurka, Mista Pompeo ya ce akalla za a iya daukar makwanni uku kafin samun kwararan sheda da har za su kai ga daukar matakin kakaba takunkumi.

Mista Kashoggi dai ba a sake jin duriyarsa ba tun da ya taka kafarsa wani ofishin jekadancin Saudiya da ke binin Santanbul na Turkiya a watan da ya gabata.

Saudiya kuma ta musanta zargin tana da hannu a kisan dan jaridar da ya yi fice wajen sukar gwamnatin kasar.

Sai dai matsin lamba daga Turkiya ya sa Saudiya ta bayyana mutane 18 da ake zargi da kisan dan jaridar.

Batun kisan dan jaridar dai na neman dagula danganta tsakanin saudiya da amniyarta Amurka.