Hotunan yadda zaman majalisar Kano da wakilin Ganduje ya kasance

Ga wasu daga cikin hotunan yadda zaman majalisar Kano da wakilin Ganduje ya kasance da aka yi a ranar Juma'a. Abokin aikinmu Ibrahim Isa ne ya dauko mana su.

Wannan ita ce kujerar da a ka shirya don gwamna Abdullahi Ganduje ya zauna a kanta
Bayanan hoto,

Da dama al'ummar da ta taru a zauren majalisar dokokin jihar Kano ta yi tsammanin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje zai je da kansa ba sako ba. Wannan ita ce kujerar da a ka shirya don gwamna Abdullahi Ganduje ya zauna a kanta

Bayanan hoto,

An dakanci isar gwaman har zuwa bayan karfe goma na safe da wasu 'yan mintoci, wato lokacin da kwamitin ya tsara don fara zaman.

Bayanan hoto,

Wannan shi ne hoton daya daga cikin mambobin kwamitin a yayin da ya ke magana

Bayanan hoto,

Amma kwatsam sai ala ga kwamishin watsa labarai, Mallam Muhammad Garba ya shiga zauren tare da lauyan Gwamna, Barrister Ma'aruf Yakasai, inda ya sanar da kwamitin cewa ya je ne ya wakilci gwamna, kasancewar gwmnan yana da zabin zuwa da kansa ko kuma a wakilce shi, inda bai tsaya wata-wata ba ya gabatar da bahasin gwamna a rubuce, wadda ya danka wa kwamitin bayan ya karanta, yana musanta zargin da ake yi wa gwamnan na karbar rashawa.

Bayanan hoto,

An tsaurara tsaro sosai a majalisar saboda sa ran zuwan gwamnan, ciki har da jami'an da ke dauke da na'urorin da ke sansanar boma-bomai.

Bayanan hoto,

Kwamitin ya bayyana kasancewar ya saurari bangarori biyun, wato da dan jaridar da ya wallafa hotunan bidiyon da kuma wanda ake zargi, yanzu kuma zai mayar da hankali ne wajen nazarin hotunan kafin ya dauki mataki na gaba.

Bayanan hoto,

Kwamitin majalisar dokokin dai na da babban kalubale a gabansa, kasancewar kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da al`umomin jihar Kano da wajen jihar da dama sun zuba masa ido wajen ganin ya kamanta adalci, kamar yadda ya yi alkawari.

Bayanan hoto,

'Yan jarida da kungiyo daban-daban sun halarci zaman.

Bayanan hoto,

Yayin da kwamitin ke fuskantar matsalin-lamba daga wasu da ke zargin cewa 'yan kwamitin 'yan-koren gwamnati ne don haka da wuya su dauki matakin da zai bakanta ran gwamna!