Yadda fadan fasinja da direba ya yi ajalin mutum 13 a China

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon ya nuna hatsaniyar ta fara kafin bas din ta fada kogin

Wani bidiyo da jami'an tsaro suka dauka ya nuna wata babbar motar bas ta fada cikin kogi a China, bayan da wani direba ya yi fada da wata fasinja yayin da motar ta sauka daga hanya.

Bas din ta fada karkashin wata gada mai zurfin mita 50 a kogin Yangtze a Chongqing, a ranar Lahadi.

Akalla mutane ne 13 suka rasa rayukansu, akwai kuma wasu biyu da ba a san inda suke ba.

Rahotannin farko sun ce bas din ta kauce ne don gudun kada ta yi karo da wata mota.

Amma sabon bidiyo ya nuna yadda wata fasinjar motar ta doki direban, sai shi ma ya rama.

'Yan sanda sun ce hadarin ya faru ne sakamakon fadan, in ji jaridar People's Daily mallakin gwamatin China.

An ji yo fasinjojin motar suna ihu a cikin bidiyon mai tashin hankali da kafar yada labaran mallakar gwamnatin kasar ta yada.

Hakkin mallakar hoto Handout
Image caption Bas din lokacin da ta kauce hanyarta

'Yan sanda sun ce fasinjar, wadda aka gano mai shekara 48 kuma mai suna Liu, ta yi fushi ne saboda bas din ta wuce inda za ta sauka.

Sun ce ta bugi direban, mai suna Ran, da wayarta, yayin da ya ki tsayawa da motar domin ta sauka.

An fara babban aikin ceto tare da kungiyoyin agaji daban-daban da kuma jiragen ruwa da yawa da aka tura.

Amma ba a samu rahotanni game da wani da ya tsira ba.

An cire motar daga cikin kogin da ke da zurfin mita 71 a ranar Laraba da daddare.

Kuma masu ninkaya sun gano yawancin gawawwakin fasinjojin.

Labarai masu alaka